Gwamnati Ta Saki Bayanai, EFCC Tana Binciken Fitaccen Minista a Mulkin Buhari

Gwamnati Ta Saki Bayanai, EFCC Tana Binciken Fitaccen Minista a Mulkin Buhari

  • Festus Keyamo ya saki sukar yarjejeniyar da Hadi Sirika ya jefa Najeriya da sunan jirgin Nigeria Air
  • Ministan harkoki da cigaban jiragen saman ya yi Allah-wadai da kwangilar, ya ce an bincike a kai
  • Lauyan ya nuna ba za a bar Hadi Sirika ya tafi haka nan ba, hukumar EFCC za ta dauki mataki

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Ministan harkoki da cigaban jiragen sama a Najeriya, Festus Keyamo ya ce EFCC tana binciken kwangilar Nigeria Air.

Ranar Alhamis The Cable ta rahoto Festus Keyamo yana cewa ana bincike a kan wannan kwangilar da ta jawo abin magana.

Hadi Sirika
EFCC: Hadi Sirika tare da Muhammadu Buhari Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Aikin kafa jiragen Nigeria Air

Hadi Sirika ya shiga wannan yarjejeniya a madadin gwamnatin Najeriya kafin Muhammadu Buhari ya bar karagar mulki.

Kara karanta wannan

A kara hakuri: Minista ya ce ana daf da cin moriyar kudurorin Shugaba Tinubu a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lamarin ya kai an dauko jirgin sama ya sauka a tashar Nnamdi Azikiwe ana saura kwanaki uku Bola Tinubu ya karbi shugaanci.

A wata hira da ya yi da tashar Channels a jiya, Ministan harkokin jiragen saman ya nuna ba za a bar maganar ta tafi a haka ba.

Gwamnatin Tinubu za ta binciki Nigeria Air

Tuni gwamnatin Bola Tinubu ta dakatar da wannan kwangila da nufin a shirya bincike.

Keyamo ya soki wannan kwangila da Hadi Sirika ya kinkimo, ya nanata cewa kafa kamfanin jirgin ba zai wani taimaki kasar ba.

"Gaba daya lamarin a hakika jirgin Ethiopian Air ne kurum yake yawo da tutar Najeriya."
"Ba jirgin gwamnati ba ne. Abubuwa biyu ne dabam. Jirgi mai daukar tuta dabam da jirgin gwamnati."
"EFCC tana binciken wannan kwangila. Ana gudanar da binciken laifi a yanzu. Na bukaci ganin rahoton.”

Kara karanta wannan

Duk da suka daga 'yan Arewa ministan Tinubu ya dage kan mayar da FAAN zuwa Legas, ya fadi dalili

- Festus Keyamo

Ministan ya ce ba za ayi amfani da jirgin gida a matsayin kamfanin gwamnati ba, yake cewa kasar za ta kafa kamfanin jirgin kwarai.

EFCC za ta kamo Hadi Sirika?

Kwanaki aka rahoto wani babba a APC ya ba Hukumar EFCC tsawon makonni biyu ta cafke tsohon Ministan jiragen sama, Hadi Sirika.

Haruna Gololo ya bukaci a damke Godwin Emefiele, Timipre Sylva da manyan da aka dama da su lokacin mulkin Muhammadu Buhari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel