EFCC Ta Fallasa Kungiyar Addinin da Ke Taimakawa Barayi Karkatar da Kudaden Sata

EFCC Ta Fallasa Kungiyar Addinin da Ke Taimakawa Barayi Karkatar da Kudaden Sata

  • Hukumar yaƙi da cin hanci ta EFCC ta yi sabuwar fallasa kan masu hannu a harkar satar kuɗaɗen jama'a
  • Shugaban hukumar, Ola Olukoyede, ya bayyana cewa sun samu wasu ƙungiyoyin addini dumu-dumu a cikin harkar
  • Shugaban ya bayyana cewa suna bincikar wata ƙungiyar addini kan zargin taimakawa wajen karkatar da N7bn na kuɗin sata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa ta'annati (EFCC), Ola Olukoyede, ya bayyana cewa hukumar ta gano wasu kuɗaɗe da aka karkatar ta hanyar amfani da wata ƙungiyar addini.

Ola Olukoyede, ya bayyana cewa kuɗaɗen da ake zargin an karkatar ɗin ta hanyar amfani da ƙungiyar addinin sun kai N7bn, cewar rahoton The Punch.

Kara karanta wannan

Duk da 'yarsa na aiki a CBN, sanatan APC ya caccaki mayar da FAAN, CBN zuwa Legas

EFCC ta tona asirin wata kungiyar addini
EFCC ta yi fallasa kan kungiyar addinin da ke taimakawa wajen karkatar da kudin sata Hoto: EFCC Nigeria
Asali: Twitter

Ya kuma bayyana cewa an gano wata ƙungiyar addini da ke yi wa ƴan ta'adda safarar kuɗaɗe, cewar rahoton jaridar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban na EFCC ya bayyana haka ne a ranar Laraba, a cibiyar Musa Yar’Adua da ke Abuja, yayin wani taro na yini ɗaya kan “matasa, addini da yaƙi da rashawa.”

EFCC ta yi fallasa kan ƙungiyoyin addini

Ya ce an gano wasu ƙungiyoyin addini, cibiyoyin addinai da malamai a ƙasar nan suna taimakawa ƴan damfara da ƴan ta’adda.

Olukoyede ya bayyana cewa EFCC ta gano N7bn da aka karkatar a asusun ajiyar banki na wata ƙungiyar addini a ci gaba da binciken badaƙalar N13bn.

Ko da yake bai bayyana sunan ƙungiyar addinin ba, wata majiya wacce take da masaniya kan batun a hukumar, ta shaida wa jaridar The Punch cewa coci ce.

Kara karanta wannan

ShIn da gaske Yahaya Bello na neman kujerar Ganduje a APC? Gaskiya ta bayyana

Shugaban na EFCC ya sha alwashin cewa hukumar za ta ƙwato ƙudaden ta hannun kotu.

EFCC Faɗaɗa Bincike Kan Badaƙalar $347bn

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa ta'annati (EFCC) tana binciken yadda aka rabawa kamfanoni $347bn a Najeriya na shekaru kusan goma.

Binciken na hukumar ya shafi abubuwan da suka faru daga watan Janairun 2014 zuwa watan Yunin 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel