EFCC: Yadda Aka Cinye Naira Biliyan 4.6 Wajen Yi wa Najeriya ‘Addu’a’ Zamanin Jonathan

EFCC: Yadda Aka Cinye Naira Biliyan 4.6 Wajen Yi wa Najeriya ‘Addu’a’ Zamanin Jonathan

  • Hukumar EFCC mai yaki da rashin gaskiya ta koma kotu da tsohon Minista, Amb. Bashir Yuguda
  • EFCC tana zargin jigon na PDP da hannu a badakalar kudin makamai da aka yi a 2014 zuwa 2015
  • Wani ma’aikaci ya halarci zaman babban kotun tarayyan, ya kuma gabatar da shaida kan Yuguda

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja – Wani jami’in hukumar EFCC, Kazeem Yusuf, ya shaidawa kotu abin da ya sani a game da badakalar kudin makamai.

Vanguard ta kawo labari cewa an cigaba da shari’ar Amb. Bashir Yuguda da hukumar EFCC a babban kotun tarayya da ke Abuja.

EFCC.
EFCC: Sambo Dasuki da Sagir Bafarawa Hoto: Sagir Attahiru Bafarawa
Asali: Facebook

EFCC ta ce addu'o'i sun ci N4.6bn a ONSA

Da aka kira Kazeem Yusuf domin bada shaida, jami’in ya ce an raba N4.6bn daga asusun ONSA da nufin ayi wa Najeriya addu’o'i.

Kara karanta wannan

EFCC ta gano kungiyar addini da ke taimakon ‘yan ta’adda

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

EFCC tana zargin Bashir Yuguda wanda ya rike karamin Ministan kudi da cin amana, karkatar da dukiya da cin dukiyar haramun.

Sauran wadanda ake tuhuma tare da tsohon ministan sun hada da Sambo Dasuki wanda ya kasance mai bada shawara a kan tsaro.

EFCC ta taso kamfanin Bafarawa a gaba

Ana kuma shari’a da Attahiru Bafarawa da yaronsa Sagir da kamfanin Dalhatu Investment Ltd wanda tsohon gwamnan ya mallaka.

Rotimi Jacobs shi ne lauyan da ya shigar da kara a madadin EFCC mai yaki da rashin gaskiya kamar yadda The Cable ta kawo rahoto.

Rotimi Jacobs ya ce sun yi bincike ne sakamakon korafi da aka samu daga ofishin ONSA.

Binciken ya nuna kamfanin Dalhatu Investment Limited yana cikin kamfanoni 78 da ake zargin an aiko masu biliyoyi daga ofishin ONSA.

Kara karanta wannan

Binani Vs Fintiri: Kotun Koli ta yanke hukunci kan shari'ar gwamnan jihar Adamawa

Tsakanin 2014 zuwa 2015, an yi ta aikawa wannan kamfani kudin da sun kai N4.6bn, Sagir Bafarawa ya tabbatar da zargin nan a rubuce.

EFCC: Ina aka kai N4.6bn?

Punch ta ce Sagir wanda ya wakilci kamfanin ya ce an yi amfani da kudin ne aka shirya addu’o’i saboda yadda rashin tsaro ya yi kamari.

Daga cikin kudin ne Sanata Abdullah Wali ya samu N580m, aka aika N322m ga Muazu Madawaki domin sayen kujerun hajji a Sokoto.

Ibrahim Maigoma ya samu N111m sai aka tura N327.5m zuwa ga Yahaya Dada, Sani Kabir ya samu N159m sannan INEC ta tashi da N293m.

Fitowar Sambo Dasuki

Bayan fitowarsa daga gidan gyaran hali a 2019, ana da labari cewa Sambo Dasuki ya ce babu wani sabani tsakaninsa da Muhammadu Buhari.

Haka zalika Kanal Dasuki mai ritaya ya shaidawa Duniya ba ya fama da wata rashin lafiya

Asali: Legit.ng

Online view pixel