Hukumar EFCC Ta Cafke Babban Malamin Addini a Najeriya, Ta Fadi Laifinsa

Hukumar EFCC Ta Cafke Babban Malamin Addini a Najeriya, Ta Fadi Laifinsa

  • Wani fasto ya shiga hannun hukumar EFCC bayan da ake zarginsa da damfarar mabiyansa da kuɗaɗen bogi daga gidauniyar Ford
  • Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta kama Apostle Theophilus Oloche Ebonyi bisa laifin almundahanar kuɗi
  • Gidauniyar Ford ta musanta "kowace irin alaƙa" da shugaban cocin ta Faith On The Rock Ministry International

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Hukumar yaƙi da yi wa tattalin arziƙin ƙasa ta’annati (EFCC) ta cafke shugaban cocin Faith On The Rock Ministry International, Apostle Theophilus Oloche Ebonyi.

Jami’an hukumar EFCC sun kama Ebonyi ne bisa laifin damfarar mabiyansa da wasu ƴan Najeriya ta hanyar amfani da tallafin jabu daga gidauniyar Ford har naira biliyan 1,319,040,274.31, cewar rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

Babbar kotu ta yanke hukunci kan buƙatar magoya bayan gwamnan PDP da ake zargi da ta'addanci

EFCC ta cafke fasto
Hukumar EFCC ta cafke fasto kan zargin damfarar mabiyansa N1.3bn Hoto: EFCC Nigeria
Asali: Facebook

Mai magana da yawun EFCC, Dele Oyewale, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Litinin, 5 ga watan Fabrairu a Abuja, kamar yadda jaridar Guardian ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Oyewale ya yi nuni da cewa za a gurfanar da Apostle Ebonyi a kotu da zarar an kammala bincike.

Yadda Ebonyi ya damfari mabiyansa

An dai bi sahun faston ne tare da ɗamke shi bisa laifin damfarar waɗanda abin ya shafa da suka haɗa da ƙungiyoyi masu zaman kansu da kuma ɗaiɗaikun mutane.

Ya cimma hakan ne ta hanyar tallata wani shiri ta hannun ƙungiyarsa mai zaman kanta (Theobarth Global Foundation) yana mai cewa gidauniyar Ford tana bayar da tallafin dala 20,000, 000. 000, domin taimakawa marasa galihu a cikin al’umma.

An ce Ebonyi yana bibiyar abokan huldarsa a wasu kafafen sada zumunta don tallata tallafin na gidauniyar Ford Foundation.

Kara karanta wannan

NFF ta fadi dalili 1 da zai sanya tawagar Super Eagles lashe kofin AFCON

Oyewale ya ce:

"An yi zargin cewa ya yaudari waɗanda abin ya shafa da su yi rajista a matsayin waɗanda za su ci gajiyar tallafin bogin ta hanyar neman su biya kuɗin fom ɗin rajista.
"Binciken da EFCC ta gudanar ya nuna cewa gidauniyar Ford ba ta da wani tsari, tallafi, dangantaka ko kasuwanci da Ebonyi."

EFCC Ta Tona Asirin Ƙungiyar Addini

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar EFCC ta bankaɗo wata ƙungiyar addini mai taimakon ƴan ta'adda a Najeriya.

Hukumar ta bayyana cewa ƙungiyar addinin tana yi wa ƴan ta'adda safarar kuɗi a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel