Kasar waje
Gwamnatin India ta sanar da mutuwar mutane 36 da kuma sama da 100 da ke wance a asibiti bayan shan giya a yankin Kallakurichi da ke jihar Tamil Nadu.
Hukumar sojojin Najeriya ta tabbatar da aniyarta na tura dakaru kasar Gambia domin taimaka mata wurin wanzar da zaman lafiya da kare lafiyar al'umma.
Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ya yi kira na musamman ga likitoci masu son tafiya kasashen ketare neman aiki kan su zauna a Najeriya.
Gwamnatin jihar Jigawa ta sanar da shirin dawo da kai dalibai kasar Singapore domin cigaba da karatu. Gwamnan jihar, Umar A. Namadi ne ya sanar da haka.
Masu aikin ceto sun gano tarkacen jirgin da ya dauki mataimakin shugaban kasar Malawi,Saulos Chilima a dajin da ya yi hatsari a kasar, kuma an tabbatar da rasuwarsa.
Babban ministan Isra'ila, Benny Gantz ya ajiye aiki bayan sabani da ya samu da firaminista Benjamin Netanyahu kan rikicin da ake tsakanin Isra'ila da Falasdinawa.
Dakta Isaac Idahosa wanda ya yi takarar mataimakin shugaban kasa ga Rabi'u Kwankwaso a jam'iyyar NNPP a zaben 2023 da aka gudanar ya samu mukami a kasar Benin.
Hukumomi a kasar Saudiyya sun tabbatar da ganin watan Dhul Hijjah a yammacin yau Alhamis 6 ga watan Yuni inda aka tabbatar da gobe 1 ga watan Dhul Hijjah.
Kasar Saudiyya ta saka taran sama da N39m ga masu zuwa aikin Hajji ba tare da izini ba. Hukumomi sun ce dokar za ta yi aiki a kan bako da dan kasa.
Kasar waje
Samu kari