Mutane Kimanin 40 Sun Mutu, Sama da 100 Suna Asibiti Bayan Sun Yi Tatul da Giya

Mutane Kimanin 40 Sun Mutu, Sama da 100 Suna Asibiti Bayan Sun Yi Tatul da Giya

  • Rahotanni da suka fito daga kasar Indiya sun yi nuni da cewa an samu asarar rayuka biyo bayan shan giyar gargajiya da mutane suka yi
  • Lamarin ya jefa al'ummar jihar Tamil Nadu cikin zaman makoki da zaman asibiti kasancewar mutane da dama na kwance rai a hannun Allah
  • Rundunar yan sandan Indiya ta yi karin haske kan halin da ake ciki tare da bayyana cewa ta kama wasu mutane da ke zargi da hannu a lamarin

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Kasar India - An samu barkewar annoba a jihar Tamil Nadu bayan mutane da dama sun sha giyar gargajiya.

Rahotanni sun yi nuni da cewa lamarin ya fara ne bayan mutane sun sha giyar a jiya Laraba, 19 ga watan Yuni.

Kara karanta wannan

Mahara sun dira Jihar Binuwai a babur, an shiga fargaba bayan kashe rayuka

Kasar Indiya
Mutane sun mutu a Indiya bayan shan giyar gargajiya. Hoto: @DrSubair_Khan
Asali: Twitter

Rahoton Daily Mail ya nuna cewa gwamnatin kasar ta tabbatar da faruwar lamarin da kuma bayyana matakin da ta dauka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Annoba a Indiya bayan shan giya

Jami'in gwamnatin Indiya ya tabbatar da cewa an samu barkewar annoba a yankin Kallakurichi da ke jihar Tamil Nadu.

Ya ce tun jiya Laraba ake samun mutane na amai da gudawa da ciwon ciki bayan shan giyar gargajiyar, rahoton BBC.

Adadin mutanen da giya ta kashe

Gwamnatin kasar ta tabbatar da cewa kimanin mutane 36 ne suka rigamu gidan gaskiya biyo bayan shan giyar.

Ta kuma bayyana cewa a halin yanzu akwai mutane sama da 100 da suke kwace a asibiti tun da suka sha giyar.

Gwamnatin kasar Indiya ta dauki mataki

Gwamnatin kasar ta tabbatar da kama mutane sama da 10 ciki har da basarake da shugaban yan sandan yankin.

Kara karanta wannan

Kano: Rundunar ƴan sanda ta yi martani kan zargin Kwankwaso na sanya dokar ta ɓaci

Hukumomin kasar sun tabbatar da kama shugabannin yankin inda suka ce an kamasu ne bisa laifin gaza hana faruwar lamarin.

Haka zalika rundunar yan sanda ta kama mutane hudu da ake zargi suna da hannu wajen samar da gurbatacciyar giyar.

An dakatar da kamfanin hako ma'adanai

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Nasarawa ta cigaba da ɗaukan matakai kan masu hako ma'adanai domin tabbatar da ingancin tsaro.

Biyo bayan haka, gwamantin ta dauki matakin gaggawa kan kamfanin Trimadix Geomin Consult Limited da ke aiki a jihar Nasarawa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng