Babban Ministan Isra’ila Ya Fadi Dalilin Ajiye Aiki Ana Tsakiyar Yaki da Falasdinawa

Babban Ministan Isra’ila Ya Fadi Dalilin Ajiye Aiki Ana Tsakiyar Yaki da Falasdinawa

  • Babban ministan Isra'ila kuma jagoran harkokin yakin kasar, Benny Gantz ya yi murabus a lokacin da suke tsaka da yaki da Falasdinawa
  • Benny Gantz ya bayyana cewa ba a son ran shi ya ajiye aikin ba sai dai kawai saboda wasu dalilai na dole da Benjamin Netanyahu ya bullo da su
  • Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya yi martani kan murabus din babban ministan cikin wani takaitaccen sako da ya wallafa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Kasar Israel - Babban ministan Isra'ila, Benny Gantz ya yi murabus daga gwamnatin Benjamin Netanyahu.

Benny Gantz ya ajiye aiki ne a yayin da aka gagara samun tsagaita wuta kan yakin da ake tsakanin Isra'ila da Falasdinu.

Kara karanta wannan

Fitaccen malamin addini, Alkali Abubakar Zariya zai ƙara aure, ya fadi sunan amaryarsa

Benny Gantz
Ministan Isra'ila ya yi murabus kan yaki da Falasdinawa. Hoto: @gantzbe
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa ministan ya sanar da jiye aiki ne a wata hira da yayi da manema labarai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ma yasa ministan ya yi murabus?

Benny Gantz ya zargi Benjamin Netanyahu da fifita manufar siyasarsa kan samun 'yancin 'yan Isra'ila 100 idan aka tsagaita wuta tsakaninsu da Falasdinawa.

Saboda haka Benny Gantz ya ce firaminista Benjamin Netanyahu yana neman hana kasar Isra'ila samun nasara saboda son zuciya.

Beeny ya buƙaci ayi zabe

A bisa dukkan alamu Benny Gantz ya dauki adawa mai zafi da gwamnatin Benjamin Netanyahu inda ya bukaci a saka ranar zabe a kasar wanda yakesa ran zai kawo ƙarshen mukin Netanyahu.

Benny ya kara da cewa ya kamata Netanyahu ya dauki matakin samar da zaben cikin gaggawa saboda kare mutuncin yan kasar Isra'ila.

Netanyahu ya yi martani ga Benny

Kara karanta wannan

Kawun tsohon ministan Najeriya, Farfesa Isa Pantami ya rasu yana da shekara 110

Firaministan Isra'ila ya yi martani ga Benny Gantz cikin wani sako da ya wallafa kan murabus din da ya yi, rahoton jaridar Leadership.

A cikin sakon, Netanyahu ya rarrashi Benny da cewa bai kamata ya yi murabus ba ganin kasar Isra'ila na cikin yaki ta ko ina.

ICC ta nemu Netanyahu ruwa a jallo

A wani rahoton, kun ji cewa babbar kotun hukunta masu manyan laifuffuka ta duniya (ICC) ta bukaci kama Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu.

Rahotanni sun nuna cewa ana zargin Benjamin Netanyahu da wasu jami'ansa ne a kan laifin kashe fararen hula a yankin Gaza a tsawon shekaru.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel