Saudiyya da UAE Sun Umarci Takaita Lokutan Sallar Juma’a, Sun Jero Dalilai

Saudiyya da UAE Sun Umarci Takaita Lokutan Sallar Juma’a, Sun Jero Dalilai

  • Hukumomi a kasashen Saudiyya da UAE da kuma Iraq sun dauki mataki kan tsananin zafi da ake fama da shi a yankin
  • Kasashen sun dauki matakin takaita lokutan sallar Juma'a domin jama'a su samu sauki yayin da ake gudanar da sallar
  • Hakan ya biyo bayan tsananin zafin da ake zargin ya yi ajalin alhazai 1,300 a kasar Saudiyya yayin aikin hajjin shekarar 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Makkah, Saudiyya - Yayin da ake ci gaba da fuskantar zafi a yankin Larabawa, hukumomi sun dauki mataki a sallar Juma'a.

Kasar Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa, UAE sun rage lokutan sallar Juma'a zuwa wasu mintuna saboda zafi.

Saudiyya ta rage lokutan sallar Juma'a saboda zafi
Saudiyya da kasar UAE sun dauki matakin takaita lokutan sallar Juma'a saboda zafi. Hoto: Saudi Gazette.
Asali: Facebook

Saudiyya ta takaita lokutan sallar Juma'a

Kara karanta wannan

Aure mai dadi: Mawaki Davido gwangwaje amaryarsa da kyautar motar alfarma

Hukumomi a Saudiyya sun rage lokacin sallar zuwa mintuna 15 kacal musamman a manyan masallatan Makkah da Madinah, cewar Arab News.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kasar ta dauki matakin ne duba da wadanda ke gudanar da sallah a waje madadin cikin masallatan, Tribune ta tattaro.

Har ila yau, kasar UAE ta umarci rage lokacin sallar Juma'a a fadin kasar zuwa mintuna 10 har zuwa farkon watan Oktoban 2024.

Kasar ta dauki wannan matakin ne domin tabbatar da kare lafiyar al'umma musamman saboda zafin a ake fama da shi.

Iran: Malamin Musulunci ya ba da shawara

Wani fitaccen malamin Musulunci a kasar Iran, Muqtada al-Sadr ya bukaci masu wa'azi su rage tsawon sallah da huduba saboda zafin da ake yi.

Malamin ya ba da wannan shawara ne domin ragewa mutane wahalar zafin rana da suke ciki musamman a yankin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai mummunan hari Masallaci, sun kashe bayin Allah a Zamfara

Kasashen Larabawa da dama dai na fama da matsalar zafi wanda ya ke illata mutane da dama musamman baki.

Rahotanni sun tabbatar da cewa akalla mahajjata 1,300 ne suka rasa rayukansu yayin aikin hajjin bana da aka gudanar a Saudiyya.

Alhazan Najeriya da suka rasu a Saudiyya

A wani labarin, mun kawo muku rahoton yadda wasu mahajjatan Najeriya suka rasa rayukansu saboda tsananin zafi.

Wasu mahajjatan kuma sun rasu ne bayan kamuwa da rashin lafiya na an kankanin lokaci yayin gudanar da aikin hajji.

A wannan rahoton, mun kawo muku cikakken sunayen mahajjatan da kuma jihohinsu da suka hada da Kaduna da Plateau da Kebbi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.