Kashim Shettima Ya Mika Bukata 1 ga Likitoci Masu Shirin Tsallakawa Kasar Waje

Kashim Shettima Ya Mika Bukata 1 ga Likitoci Masu Shirin Tsallakawa Kasar Waje

  • Mataimakin shugaban kasa Sanata Kashim Shettima ya gana da kungiyar likitoci ta kasa (NMA) a fadar shugaban kasa a Abuja
  • Yayin ganawar, Sanata Kashim Shettima ya yi kira ga shugabannin kungiyar kan kaucewa guduwa ƙasashen waje neman aiki
  • Shugaban kungiyar, Farfesa Bala Audu ne ya jagoranci tawaga ta musamman domin ganawa da mataimakin shugaban kasar

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ya shawarci likitoci kan yin aiki a Najeriya.

Sanata Kashim Shettima ya ce ya kamata kungiyar likitoci ta kasa (NMA) ta yi yaki da ɗabi'ar guduwa ƙasashen ƙetare da wasu ƴaƴanta ke yi.

Kara karanta wannan

Kashim Shettima ya bayyana yadda Tinubu ya gina Atiku da sauran mutane a siyasa

Kashim Shettima
Kashim Shettima ya ce akwai bukatar likitoci su tsaya a Najeriya maimakon tafiya ketare. Hoto: Kashim Shettima
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa kungiyar likitocin ta gana da mataimakin shugaban kasar ne a jiya Laraba a Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shettima yana so likitoci su inganta kasa

Yayin ganawa da kungiyar likitoci ta kasa, Sanata Kashim Shettima ya ce ya kamata likitoci su kawar da kai ga guguwar tsallakewa ƙasashen ketare.

Sanata Kashim Shettima ya ce tsayawa a gida domin gina kasa mai inganci shi ne yafi sama da zuwa waje domin gina kasar wasu.

Shugaba Tinubu zai inganta harkar lafiya

Sanata Kashim Shettima ya yiwa kungiyar likitocin albishir da cewa shugaba Bola Tinubu yana ƙoƙarin inganta walwalarsu, rahoton Channels Television.

Ya kara da cewa akwai karin tanadi da shugaban kasa Bola Tinubu ya ke da shi ga likitocin da suka zabi su tsaya a gida Najeriya.

"Ya kamata mu zama kwararru" - Shettima

Kara karanta wannan

"An maida rai ba komai ba," Atiku ya riga shugaban kasa ta'aziyyar kisan Katsina

Har ila yau, Sanata Kashim Shettima ya yabi kokarin da likitoci suke yi a Najeriya wajen inganta harkar lafiya.

Amma duk da haka ya yi kira ga kungiyar kan cigaba da karfafa masu karantar likitanci domin su zama kwararru a aikin su.

Shettima ya yabi Bola Tinubu

A wani rahoton, kun ji cewa mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya ce shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ne gwarzon dimokuraɗiyya a Najeriya.

Sanata Kashim Shettima ya ce Bola Tinubu ya taimaki manyan yan siyasa a Najeriya ciki har da babban abokin hamayyarsa, Atiku Abubakar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng