"Ba Za Mu Saurarawa Isra'ila ba, ba Za Mu Daga Kafa ba," Inji Shugaban Hezbollah

"Ba Za Mu Saurarawa Isra'ila ba, ba Za Mu Daga Kafa ba," Inji Shugaban Hezbollah

  • Yayin da kasar Isra'ila ke barazanar kai hari kasar Lebanon, kungiyar Hezbollah ta ce babu abin da zai girgiza su wajen tabbatar da sun yi raddi
  • Jagoran Hezbollah, Sheikh Hassan Nasrallah ne ya yi gargadin, inda ya ce sun shirya gwabza kazamin yaki da Isra'ila matukar ta kai babban hari kan kasarsu ta Lebanon
  • Hassan Nasrallah ya kara da cewa Isra'ila da Kawayenta na sane da yadda Hezbollah ta shirya, shi ne ma abin da ya tsorata ta har ta gaza kai masu wani mummunan hari

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Lebanon- Kungiyar gwagwarmaya ta Hezbollah da ke Lebanon ta ce duk wasu nau'in tsoratarwa da yada labaran yaki a Isra'ila da kawayenta ba zai girgiza su ba.

Kara karanta wannan

Mahara sun dira Jihar Binuwai a babur, an shiga fargaba bayan kashe rayuka

Shugaban kungiyar, Hassan Nasrallah ne bayyana haka biyo bayan jawabin da Isra'ila ta yi na cewa ta shirya yakar Lebanon.

Hezbollah
Hezbollah ta gargadi Israila da kawayenta Hoto: francesca volpi
Asali: Getty Images

A wani labari da ya kebanta da Aljazeera, Hassan Nasrallah ya ce za su yaki Isra'ila ba tare da martaba wasu dokoki ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Mun shirya yakar Isra'ila," Hezbollah

Kungiyar gwagwarmaya ta Hezbollah ta bayyana cewa "makiyanta sun sani cewa a shirye ta ke wajen yakar Isara'ila.

Shugaban Hezbollah, Hassan Nasrallah ya ce ba za su saurara ba matukar Isra'ila ta kai gagarumim hari kan kasar Lebanon.

Ya ce:

"Sun san mun shirya, shiri mai kyau, shi yasa suka gaza tunkarar mu har na tsawon watanni tara."
"Idan aka fara yakar Lebanon, masu gwagwarmaya (Hezbollah) za su yi raddi."

- Hassan Nasrallah, shugaban Hezbollah

Hezbollah ta rama harin Isra'ila

Kara karanta wannan

Jagoran IPOB, Nnamdi Kanu ya saduda, ya nemi ayi sulhu da gwamnati

A wani labarin kun ji cewa kungiyar Hezbollah ta kai harin ramuwar gayya kan Isra'ila bayan ta kai wani hari kan Mais al-Jabal, da ke kudancin Lebanon inda ta ce za ta ci gaba da yakar kasar.

Kungiyar ta bayyana cewa ta harba rokoki yankin Mais al-Jabal, da ke kudancin Lebanon, kuma ba za su tsagaita wuta ba har sai Isra'ila da dakatar da harin da take kaiwa Falasdinu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.