Bello Turji
Yan bindiga sun sake kai muggan hare-hare a wasu yankunan Sokoto inda aka yi ajalin mutane wanda ake zargin yaran Bello Turji da daukar nauyin harin.
Rahotanni da muke samu sun tabbatar da cewa ƴan bindiga da ake zargin yaran Bello Turji ne sun kai farmaki garuruwa da ke karamar hukumar Isa a Sokoto.
Wasu rahotanni sun ce hare-haren sojoji a Danjibga da wasu dazukan Kudancin Zamfara na tilasta wa 'yan bindigar guduwa daga maboyarsu a Zamfara zuwa Sokoto.
Yayin da ake ta kokarin dakile matsalar tsaro a Arewa, Sheikh Murtala Bello Asada ya sake tasowa da bayanai kan yadda matsalar tsaro ke ƙara kamari a yankin.
Wasu rahotanni sun tabbatar da cewa 'yan bindiga sun kai farmaki a Rijiya da ke Zamfara, inda suka kashe mutane takwas tare da kona wata makarantar firamare.
Mazauna karamar hukumar Isa, da ke jihar Sakkwato sun gamu da iftila'in harin ƴan ta'adda, bayan Bello Turji da jama'arsa suka kai masu farmaki, an kashe mutane.
Ministan tsaron Nkasar nan, Alhaji Badaru Abubakar ya bayyana cewa Najeriya ba za ta ci gaba da zuba idanu a kan rashin tsaron da ya addabe ta ba.
Babbar kotun tarayya da ke Abuja, a karkashin Mai Shari'a, Emeka Nwite ta haramta beli ga wasu mutane da ake zargin suna da alaka da Bello Turji.
Rahotanni sun tabbatar da cewa yan bindiga da ake zaton yaran Bello Turji ne sun sace wani mutum da ya bayyana kansa a bidiyo a matsayin ɗan Ishyaka Rabiu.
Bello Turji
Samu kari