Ba Kamar Ganduje Ba, Ministan Tinubu Ya Amince Ya Yi Aiki Tare da Gwamnan Jiharsa, Ya Fadi Dalili

Ba Kamar Ganduje Ba, Ministan Tinubu Ya Amince Ya Yi Aiki Tare da Gwamnan Jiharsa, Ya Fadi Dalili

  • Bello Matawalle, Karamin Ministan Tsaro a Najeriya ya yi alkawarin aiki tare Da Gwamna Dauda Lawal don ciyar da jijar gaba
  • Matawalle ya ce a shirye ya ke a matsayin Minista a ma'aikatar tsaro don ba da gudunmawa wurin inganta tsaro a jihar da Arewacin Najeriya
  • Wannan na zuwa ne bayan Gwamna Dauda Lawal ya yi nasara a Kotun Koli a ranar Juma'a 12 ga watan Janairu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Zamfara - Karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle ya amince ya yi aiki tare da Gwamna Dauda Lawal na Zamfara.

Matawalle ya ce sun karbi hukuncin Kotun Koli hannu bibbiyu kuma su na yi wa Gwamna Dare fatan alkairi.

Kara karanta wannan

Bayan sha da kyar a Kotun Koli, gwamnan Arewa ya yi alfaharin shi jarumi ne ba ya tsoron artabu

Matawalle ya tura sako ga Gwamna Dauda Lawal kan matsalar tsaro
Matawalle Ya Amince Ya Yi Aiki Tare da Gwamna Dauda Lawal. Hoto: Dauda Lawal Dare, Bello Matawalle.
Asali: Twitter

Mene Matawalle ke cewa ga Dauda Lawal?

Ministan ya bayyana haka ne yayin hira da DCL Hausa inda ya ce zai ba da dukkan gudunmawa don ci gaban jihar Zamfara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

"Ina kira ga Gwamna Dauda Lawal ya rike duk dan jihar Zamfara ba tare da bambanci ba.
"Yanzu siyasa ta wuce ya kamata mu hada kai don samar da tsaro a jihar Zamfara kuma ina fata a wannan lokaci na shi a kawo karshen matsalar tsaro.
"A matsayin na Minista a ma'aikatar tsaro zan ba da dukkan gudunmawa don tabbatar da tsaro a Zamfara da Arewacin Najeriya da ma Nigeria baki daya."

Wace shawara Matawalle ya bai wa Dauda Lawal?

Matawalle ya bukaci gwamnan da ya dauki kowa dan uwansa a sha'anin Zamfara inda ya shawarce shi da ya guji wasu shawarwari da ba su dace ba.

Kara karanta wannan

"Kada ku tsinewa shugabanninmu": Sarkin Musulmi ya aika muhimmin sako ga yan Najeriya

Wannan na zuwa ne bayan Bello Matawalle wanda ya yi takara a jam'iyyar APC ya gaza yin nasara a Kotun Koli.

Gwamna Dauda Lawal ya tabbata zababben gwamnan jihar bayan Kotun Daukaka Kara ta rusa zaben a matsayin wanda bai kammala ba.

Abba Kabir ya bukaci hadin kai daga Gawuna, Ganduje

A wani labarin, Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya nemi yin aiki tare da dan takarar jam'iyyar APC, Nasiru Gawuna a jihar.

Wannan na zuwa ne bayan gwamnan ya yi nasara a Kotun Koli da ta tabbatar da nasararsa a matsayin gwamnan jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel