Akwa Ibom
Gwamnatin Akwa Ibom ta yi alkawarin biyan matan da suka haifi 'yan biyu naira dubu 50 duk wata yayin da wadanda suka haifi 'yan uku za su samu naira dubu 100.
Jam'iyyar YPP a jihar Akwa Ibom ta rushe gaba daya tsarinta a cikin jam'iyyar APC. Sun dauki matakin ne domin yin mubaya'a ga shugaban majalisar dattawa, Akpabio.
Kotun daukaka kara mai zama a babban birnin tarayya Abuja ta rushe nasarar Emmanuel Ukpong-Udo, mamban majalisar wakilan tarayya daga jihar Akwai Ibom.
Kotun Koli ta tabbatar da nasarar Gwamna Umo Eno na jihar Akwa Ibom a matsayin zababben gwamnan jihar, ta yi fatali da korafe-korafen APC da NNPP.
Tsohon hadimi a gwamnatin Muhammadu Buhari, Sanata Ita Enang ya gurfana a gaban Babar Kotun Tarayya kan zargin bata wa tsohon gwamnan Akwa Ibom suna.
Shugaban cocin INRI Spiritual Evangelical, Primate Babatunde Elijah Ayodele, ya yi hasashen ficewar Gwamna Umo Eno daga jam'iyyar PDP zuwa jam'iyyar APC.
Kamfanin da ake zaton babu kamarsa a faɗin Nahiyar Afirka a ɓangaren kera allura da sirinji ya rufe ofishinsa na Najeriya saboda abinda ya kira yanayin kasuwanci.
Mai shari'a Joy Unwana alkaliyar kotu a jihar Akwa Ibom wacce yan bindiga suka sace ta kubuta. Gwamna Eno na jihar ya yi tsokaci kan kubutar alkaliyar.
Wasu yan bindiga da ba a tantance ko su wanene ba sun yi garkuwa da wata alkaliyar kotu a jihar Akwa Ibom a ranar Litinin, sun kuma kashe dan sanda mai tsaronta.
Akwa Ibom
Samu kari