Emefiele: Shugaban Majalisar Dattawa Ya Ambaci Mutumin da Ya Jefa Kowa a Matsin Tattali

Emefiele: Shugaban Majalisar Dattawa Ya Ambaci Mutumin da Ya Jefa Kowa a Matsin Tattali

  • Godwin Emefiele shi ne wanda ya jawo duk wani matsin lambar tattalin arzikin da ake kuka a kai a cewar Godswill Akpabio
  • Shugaban majalisar dattawan kasar ya ce an tafka barna musamman a bankin CBN kafin Bola Tinubu ya zama shugaban Najeriya
  • Sanata Godswill Akpabio ya ce gwamnatin Tinubu ta san yadda za ta gyara kasa, ya roki talakawa suyi hakuri da mulkin APC

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Rivers - Godswill Akpabio ya koka a game da yadda Godwin Emefiele ya rike babban bankin Najeriya a shekarun da ya yi yana gwamnan CBN.

Daily Trust ta rahoto shugaban majalisar dattawan yana cewa Godwin Emefiele ya bar tattalin arzikin Najeriya a wani mummunan yanayi.

Kara karanta wannan

Sanatan Arewa ya tsarge Minista da Gwamnan CBN da ya soki manufofin Tinubu a bidiyo

Emefiele
Godwin Emefiele ya gamu da sukar Sanata Godswill Akpabio Hoto: Nigerian Senate
Asali: Facebook

Duk halin da ake ciki a yau na matsin lamba da kunci, Godswill Akpabio yana ganin Emefiele da aka dakatar daga CBN yana da hannu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban majalisar ya yi wannan ikirari ne a wajen taron addu’o’in da aka shiryawa Sanata Barinada Mpigi a karamar hukumar Tai.

Akpabio ya ce Tinubu zai gyara tattali

Da aka nemi Sanata Akpabio ya yi jawabi, sai ya tabbatarwa ‘yan Najeriya cewa gwamnatin Bola Tinubu za ta farfado da tattali.

The Cable ta ce tsohon gwamnan na Akwa Ibom ya ce Bola Tinubu ya san yadda zai magance matsalolin da aka zabe sa domin ya gyara.

Shekaru 60 ana barna kafin Tinubu

Babban ‘dan siyasar ya ce an dauki fiye da shekaru 60 ana barna, saboda haka ba za a iya shawo kan tabargazar a watanni shida ba.

Kara karanta wannan

Atiku ya fadi yadda Tinubu ya haddasa tashin Dala da rugujewar tattali a wata 8

Kamar yadda ake kira, Akpabio ya nemi mutane su kara hakuri da gwamnatin Tinubu.

Jawabin Godswill Akpabio a Ribas

“Saboda haka irin bashi da kwamacalar tattalin arzikin da mu ke ciki a yau, da yawa ba za su fahimta ba”
“Amma na tuna shugaba Barack Obama yana cewa ba za ka san Washington ba sai ka shigo Washington.”
“A lokacin da mu ka duba yanayin tattalin arzikin kasar nan, abin ya yi muni sosai.”
“Kun san ba mu san laifin da za mu kama tsohon gwamnan bankin CBN da aikatawa ba.”

- Godswill Akpabio

A yayin da ake fama da yunwa, Sanatan ya zargi Emefiele da rike makamai babu izini da kuma buga kudi ba tare da bin doka ba.

Sanata ya soki manufofin Tinubu

Rahoton nan ya zo cewa Muhammad Sani Musa ya yi tir da yadda bankin CBN ya karya darajar Naira bayan nada Yemi Cordoso.

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya tona yadda Gwamnatin Buhari ta ‘saida’ man shekaru masu zuwa

Sanata Muhammad Sani Musa ya ce babu kasa mai hankali da za tayi haka a Duniya sai kasashe marasa karfi irinsu Zimbabwe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel