Ana Cikin Jimamin Mutuwar Jarumar Fina-finai, Gwamna Ya Bukaci Tono Gawarta Daga Kabari

Ana Cikin Jimamin Mutuwar Jarumar Fina-finai, Gwamna Ya Bukaci Tono Gawarta Daga Kabari

  • Yayin da ake jimamin mutuwar jaruman Nollywood guda hudu, gwamnan jihar Akwa Ibom ya bukaci tono wata gawa daga cikinsu
  • Gwamna Umo Eno ya dauki matakin ne domin yin biki na musamman da kuma binne gawar cikin gata sabanin yadda aka binne ta
  • Gwamnan ya umarni tono gawar jarumar mai suna Abigail Edith Frederick bayan an binne ta a bakin kogi saboda rashin kuɗi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Akwa Ibom - Gwamna Umo Eno na jihar Akwa Ibom ya jajantawa iyalan jarumar fina-finai, Edith Frederick.

Gwamnan ya tura sakon jajen ne bayan rasuwar jarumar a hatsarin jirgin ruwa a jihar Anambra da sauran jarumai, cewar Leadership.

Kara karanta wannan

Kano: Abba Kabir ya dauki zafi bayan sakin 'yan daba daga kulle, ya sha alwashi kan lamarin

Gwamna ya ba da umarnin tono gawar jarumar fina-finai
Gwamna Umo Eno na Akwa Ibom ya umarci tono gawar jarumar fina-finai domin yi mata gata. Hoto: Umo Eno.
Asali: Facebook

Musabbabin tono gawar jarumar

Mutuwar jarumar ke da wuta aka binne ta a bakin kogin saboda iyayenta ba za su iya daukar nauyin binne ta ba tare da gudanar da biki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin haka gwamnan ya ba umarnin tono gawarta domin yi mata biki na musamman tare da binne ta cikin gata, cewar rahoton Tribune.

Sakataren yada labaran gwamnan, Ekerete Udoh shi ya bayyana haka inda ya ce matashiyar ta na da kwazo kuma ta cancanci biso mai daraja.

Gwamna ya tura sakon jaje ga iyalanta

"Daya daga cikin wadanda suka mutun, Abigail Edith Frederick ta kasance matashiya mai kwazo wacce ba ta wuce shekaru 24 ba a duniya."
"Mun kadu da samun labarin rasuwarta, muna mika sakon jaje ga iyalanta da 'yan uwa da kuma masana'antar Nollywood."
"Mun samu labarin yadda aka binne ta, tabbas gwamnati ba ta samu labarin yadda lamarin ya kasance ba."

Kara karanta wannan

Fusatattun Yarbawa na son a raba Najeriya, sun farmaki sakateriyar gwamnati a Oyo

"Gwamna Umo Eno ya ba da umarnin tono gawarta domin yi mata biki da sake binne ta cikin gata."

- Ekerete Udoh

Jarumai 4 sun mutu a hatsari

A baya, mun kawo muku labarin cewa wasu jaruman fina-finan Nollywood guda hudu sun mutu a hatsarin jirgin ruwa a jihar Anambra.

Cikin jaruman akwai Junior Pope wanda ya yi fice cikin jaruman inda ya farfaɗo kafin daga bisani ya ce ga garinku.

Mutuwar jaruman guda hudu ya tayar da hankulan mutane musamman ganin irin mutuwar da suka yi a cikin kogi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel