Abun Bakin Ciki
Mazauna Gatawa da ke a Sabon Birni, jihar Sokoto sun mika lamuransu ga Allah yayin da suka dukufa da yin addu'o'in kubutar Sarkin Gobir daga hannun 'yan bindiga.
Cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta Najeriya (NCDC) ta ce an sami rahoton bullar cutar kyandar biri a mutane 39 yayin da ta dauki matakan gaggawa.
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa NEMA, zayyano sunayen kananan hukumomi 14 na jihar Kano da ke fuskantar hadarin ambaliyar ruwa a daminar bana.
Abokan huldan bankin GT sun shiga dimuwa bayan wasu da ake zargi 'yan damfara ne sun yi kutse a yanar gizon bankin a yau Laraba da ya jawo matsala.
Basarake a Takum da ke jihar Taraba, Barista Sopiya Ahmadu Gboshi ya nuna damuwa kan rasa rayuwa a yankin inda ya zargi yan jihar Benue da kara rashin tsaro.
Hukumar tsaron fararen hula NSCDC ta tabbatar da mutuwar wasu matasa biyu bayan sun nutse a kududdufi a yankin karamar hukumar Birnin Kudu a Jigawa.
Kimanin mutane bakwai ne 'yan bindiga suka kashe a kauyen Sai da ke jihar Taraba. An ruwaito cewa wasu fusatattun matasa sun yi harin ramuwar gayya.
Rahoto ya nuna cewa wasu miyagun 'yan bindiga sun yi ajalin wani jajurtaccen jami'in sojin Najeriya, Kyaftin Ibrahim Yohana watanni tara kacal bayan aurensa.
Kotun Magistrate da ke jihar Ondo ta daure basarake mai daraja da ake kira Francis Ogundeji a gidan kaso har na tsawon shekaru uku saboda saba umarnin kotu.
Abun Bakin Ciki
Samu kari