Lauya Ya Ga Hannun Tinubu wajen Neman Hana Pantami da Aminu Gwarzo Shiga Takara
- Abba Hikima Esq. bai cikin masu ganin doka ce ta ke neman hana wasu jam’iyyu shiga takarar gwamna
- Lauyan kuma mai kare hakkin bil adama ya ce gwamnatin Bola Tinubu tana yin yadda ta ga dama a kotu
- Hikima yana zargin cewa dama ‘yan majalisa sun zama ‘yan amshin shatan shugaban kasa a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Kano - Abba Hikima Esq. yana ganin cewa matsalolin da suke damun wasu ‘yan takara ba tsautsayi ba ne, tuggun siyasa ne.
Matashin lauyan ya tofa albarkacin bakinsa game da abubuwan da suka faru da ‘yan adawa wajen neman takarar gwamna.

Source: Twitter
A wani rubutu da yake shafinsa a Facebook, Abba Hikima ya zargi gwamnati da jefa NDC da PDP a matsala a Kano da Gombe.
Yake cewa akwai hanyoyi hudu da jam’iyya mai mulki da gwamnatin Bola Tinubu ta ke bi wajen dasa matsalolin takara.
Abba Hikima ya jefi gwamnati da manyan zargi
Lauyan ya ce:
"Abin da ya samu NDC a Kano, PDP a Gombe da mafi yawan matsalolin da jam’iyyu da yan takarkarin adawa suke samu a yanzu, kada ka raba ɗaya biyu, kitumurmurar shugabancin Tinubu da jam’iyyar APC ne.'
Hikima ya ce an fara yin wannan ne da aka karbe ta-cewar majalisa ta hanyar samun shugabannin da ke tare da gwamnati.
Baya ga rufe bakin sanatoci da ‘yan majalisar wakilan tarayya, Hikima yana ganin wata dabarar tana cikin gyaran dokar zabe.
Idan maganarsa ta tabbata, an yi wasu cushe-cushe wajen yi wa dokar zabe garambawul, wannan ya kara wa INEC karfi.
Dabara ta uku da ya yi zargin an yi shi ne an kawo sabon shugaban hukumar INEC da ake so.
Tun da aka nada Farfesa Jaoah Amupitan ya jagoranci hukumar zabe aka fara ji wasu musamman a Arewa suna kuka da shi.
Ana sayen shari'a a gwamnatin Tinubu?
Da aka yi kane-kane a majalisun tarayya da INEC, lauyan ya ce sai gwamnatin Tinubu ta shiga cikin sha’anin shari’a a kotuna.
Fitaccen ‘dan gwagwarmayan yana da tunanin cewa idan shari’ar siyasa ta je kotu, babu tabbacin alkalai za su yi gaskiya.
Rubutun ya kawo misalan manyan alkalan da suka gaskata maganar shi, suka ce ana aiki da kudi wajen sayen shari’a a kotu.
Rubutun da Abba Hikima ya yi a Facebook
"An yi wannan ta hanyoyi 4.
"Na farko, yadda fadar shugaban ƙasa ta tabbatar da samun shugabancin majalisun dattawa da wakilai. Kowa ya san yadda wannan abu ya faru. Burin su su samu yan amshin shata. Kuma sun samu.
"Na biyu, gyaran da su masu yin dokar suka yi wa dokar zaɓe na ba gaira ba dalili a shekarar nan. Suka cusa wasu sassa da suka ƙarawa hukumar zaɓe (INEC)wani irin ƙarfi na musamman.
"Na uku, sai aka zaɓo shugaban INEC da suke so. Kowa ya san dambarwar da aka yi akan sa. Yanzu tunda sun samu yan majalisa sun musu dokar zabe, sai su samu masu zartar wa waɗanda suke so su musu abunda suke so.
"Na hudu, kotuna. Sun san duk lokacin da INEC ta ɓatawa mutane ko jam’iyyu, abu na gaba shine a kai ƙara kotu. Duk da kotunan Nigeria a rubuce zaman kansu suke yi, ina tabbatar muku duk shari’un da suke shafi siyasa sai kawai abunda ka gani. Wannan hatta manyan alƙalan koton Koli irin su Amina Augie JSC rtd. da Muhammad Dattijo JSC rtd. sun tabbatar da wannan a bainar jama’a. Sharia da ƙuɗi ma siyan ta ake yi ballantana da ƙarfin mulki ko barazana."
- Abba Hikima
A karshe ya ce idan wani abin tuhuma ya faru nan gaba, ba laifin kowa ba ne illa Tinubu da jam'iyyar APC.
"Saboda haka, duk abin da kuga gani mara dadi daga kotuna, INEC ko majalisa, kada kiyi wani biye-biye, ku zargi shugaba Tinubu da jam’iyyarsa."
Jam'iyyar APC ta yi hankali a Legas
Ana da labari cewa APC za ta ƙara ƙaimi wajen neman ƙuri’u saboda gudun a kara kunyata Bola Tinubu a gidansa, jihar Legas.
Peter Obi, ya samu kuri’u 582,454, yayin da ‘dan takaran APC ya tashi da 572,606 a 2023, hakan bai yi wa jam'iyya mai-ci dadi ba.
APC ta yi wa mambobi kusan miliyan 1 rajista, ana sa ran za su zabi Tinubu da Kadri Hamzat ya zama gwamnan jihar Legas
Asali: Legit.ng


