Mutuwar Kusan Mutum 100 Lokaci Guda Ya Girgiza Gwamnan Kano, Abba Ya Aika Saƙo

Mutuwar Kusan Mutum 100 Lokaci Guda Ya Girgiza Gwamnan Kano, Abba Ya Aika Saƙo

  • Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya jajanta wa gwamnatin Neja da iyalan waɗanda suka rasa rayukansu a fashewar tankar mai
  • Gwamnan ya jaddada muhimmancin wayar da kan jama’a kan haɗarin dibar fetur daga wurin da tanka ta yi hatsari, ya ba hukumomin shawara
  • Wani mummunan hatsarin tanka a Dikko Junction, kan titin Abuja-Kaduna, ya yi sanadin rasuwar mutane 98, ciki har da mata masu ciki da yara

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano - Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, a ranar Litinin, ya miƙa saƙon ta’aziyya ga gwamnatin jihar Neja kan mummunar fashewar tankar mai da ta faru a Dikko Junction.

Tun farko tankar ta yi hatsari a kan titi, mutane suka baibayeta suna ɗibar man fetur, ba zato wuta ta kama ta rutsa gaba ɗaya mutanen da suka cika wurin.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta yi kuskuren ingiza wa wani jami'inta maƙudan kuɗi, ya dawo da su

Gwamna Abba da Umaru Bago.
Gwamnan Kano ya yi ta'aziyya ga gwamnatin Neja da al'umma bisa rasa rayuka sakamakon fashewar tanka Hoto: Sanusi Bature D-Tofa, Mohammed Umaru Bago
Asali: Facebook

Mutane kusan 100 sun mutu a fashewar tanka

Wannan lamari mai ban tausayi, wanda ya faru a safiyar Asabar, zuwa yanzu ya yi sanadin mutuwar akalla mutane 98, ciki har da wata mai juna biyu da yara masu yawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan Kano ya miƙa sakon ta'aziyya ga gwamnati da al'ummar jihar Neja bisa wannan iftila'i da ya faru tare da addu'ar Allah ya jiƙan waɗanda suka rasu.

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin-Tofa, ya wallafa a shafinsa na Facebook yau Litinin

Rahotannin ganau sun nuna cewa waɗanda lamarin ya shafa sun kone ƙurmus ta yadda ba za a iya gane su ba.

Gwamnan Kano ya yi alhinin faruwar lamarin

Gwamna Abba Yusuf ya bayyana wannan ibtila'i da ya yi ajalin kusan mutum 100 a matsayin babbar jarabawa da ta shafi kowane ɗan ƙasa.

Abba, wanda ya nuna takaicinsa saboda za a iya guje wa irin wannan lamari, ya yi kira da a ɗauki matakan gaggawa don hana irin wannan faruwa a gaba.

Kara karanta wannan

An shiga jimami bayan tankar mai ta sake fashewa a Najeriya, mutane 11 sun rasu

“A madadin gwamnatin da mutanen Kano, ina miƙa ta’aziyya ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu da kuma gwamnatin jihar Neja.
"Muna alhinin tare da addu’ar Allah ya ji ƙan waɗanda suka rasu kuma ya ba wa waɗanda suka ji rauni sauƙi cikin gaggawa.”

Gwamna Abba ya ba hukumomi shawara

Gwamnan ya jaddada muhimmancin wayar da kan jama’a kan haɗarin ɗebo mai daga wuraren da hatsari ya faru.

Ya kuma yi kira ga hukumomin da ke da alhaki su tabbatar ana bin dokoki da ƙa'idojin tsaro a manyan hanyoyi don kare rayuka da dukiyoyin al'umma.

Abba ya sake nanata ƙudurinsa na goyon bayan yunkurin da zai inganta tsaron rayuka da jin daɗin al’umma, yana mai kira ga ‘yan Najeriya su kasance masu lura da taka-tsantsan.

“Allah ya ji ƙan waɗanda suka rasu kuma ya ba iyalansu ƙarfin ikon jure wannan babban rashi,” in ji Gwamna Abba.

Shugaba Tinubu ya miƙa sakon ta'aziyya

Kara karanta wannan

Su waye ke daukar nauyin ta'addanci? Hafsan tsaro ya fayyace gaskiya kan lamarin

A wani labarin, kun ji cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi jimamin rasa rayuka a fashewar tankar da ya afku a jihar Neja.

Shugaba ƙasar ya nuna alhininsa ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu a wannan hatsari mai tayar da hankali.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262