Abun Bakin Ciki
An tashi da mummunan labarin rasuwar Sheikh Muhammadu Kobuwa a Gombe, shehin malamin ya rasu ne a yau Juma'a 9 ga watan Faburairu a birnin Gombe.
Dalibai biyu na kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar Kogi, Lokoja sun mutu sakamakon shakar hayakin da ke fitowa daga janareta da ke kusa da tagar dakunansu.
Shahararriyar jarumar fina-finan Nollywood, Ethel Ekpe ta riga mu gidan gaskiya a jiya Laraba 7 ga watan Faburairu a Legas bayan ta sha fama da jinya.
Basaraken gargajiya na Asaba, babban birnin jihar Delta, Mai martaba Obi (Prof.) Joseph Chike Edozien, ya rasu, a yayin da yake shirye-shiryen bukin cika shekaru 100
Babban jigon jam’iyyar APC a jiha Delta, Cairo Ojougboh, ya yanke jiki ya mutu yayin kallon wasan kwallo tsakanin Najeriya da Afrika ta Kudu a gasar AFCON 2023.
A jiya ne masoya harkokin wasanni a Najeriya suka shiga cikin makoki yayin da wani fitaccen dan jaridan wasanni Kayode Tijani ya rasu bayan fama da jinya a asibiti.
Rundunar ‘yan sandan Najeriya, ta tabbatar da cafke Aisha Jibrin da wasu mutane 25 da ake zargi da hannu a zanga-zangar da aka yi a Minna, jihar Neja.
Hukumar Jami'ar jihar Kano, ta Aliko Dangote da ke Wudil ta dauki mataki kan wani lakcara da ya hukunta dalibai a cikin aji tare da saka su tsallen kwado.
Allah ya karbi rayuwar Farfesa Yusuf Dankofa a jihar Kaduna ya na da shekaru 61 a duniya, kafin rayuwarsa ya na daga cikin lauyoyin Atiku Abubakar a zaben 2019.
Abun Bakin Ciki
Samu kari