"Ba Yi Niyya ba"; Matashi Ya Yi Wa Budurwarsa Danyen Aiki bayan Ta Ziyarce Shi har Gida
- Rundunar ’yan sandan Edo ta kama Miracle Samuel mai shekara 21 bisa zargin yi wa budurwarsa mummunan abu
- Kwamishinan ’yan sanda ya ce wanda ake zargin ya gayyaci budurwar zuwa gidansa da ke yankin Ahor a Benin City, inda ake zargin ya kashe ta da wuƙa
- Matashin ya ce bai yi niyyar kashe budurwar ba, yana mai cewa ta ji rauni ne yayin da suke kokawa kan wuƙa bayan sun samu saɓani
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Edo - Rundunar ’yan sandan jihar Edo ta kama wani matashi mai suna Miracle Samuel, mai shekara 21, bisa zargin kashe budurwarsa wadda ya haɗu da ita a kafar sada zumunta.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, Patrick Daaor, ya bayyana cewa matashin da budurwar sun haɗu ne ta intanet, inda suka fara abota bayan sun shafe watanni suna tattaunawa.

Source: Facebook
A cewarsa, daga baya wanda ake zargin ya gayyaci budurwar zuwa gidansa da ke yankin Ahor a birnin Benin, inda ake zargin ya kashe ta da wuƙa, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
Daaor ya ce a halin yanzu ana tsare da matashin a hannun ’yan sanda, kuma za a gurfanar da shi a gaban kotu bayan kammala bincike.
Abin da matashin ya ce kan lamarin
Sai dai a wata hira da aka yi da shi, Miracle Samuel ya ce bai yi niyyar kashe budurwar tasa ba, yana mai cewa ta ji rauni ne a lokacin da suke kokawa domin ƙwace wuƙa.
Ya yi zargin cewa budurwar ta yi ƙoƙarin amfani da wuƙar wajen soka masa bayan sun samu saɓani.
“Ban yi niyyar kashe ta ba, amma ta ji rauni ne a lokacin da muke kokawa kan wuƙar yayin da muke gardama,” in ji shi.
Matashin ya ce sun haɗu ne a kafar sada zumunta, inda suka fara abota bayan tattaunawa na tsawon watanni. Ya ƙara da cewa daga baya budurwar ta yanke shawarar zuwa gidansa domin ziyara.

Kara karanta wannan
Abin bakin ciki: Matashi ya kashe abokinsa da suke aiki wuri 1 kan gardamar siyasa
Yadda gardamar ta rikide muwa mummunan lamari
Samuel ya bayyana cewa a ranar da budurwar ta ziyarce shi, suna tattaunawa ne kafin tattaunawar ta rikide zuwa gardama.
Ya yi zargin cewa a lokacin gardamar, budurwar ta ɗauki wuƙa da niyyar soka masa.
“A ranar da ta zo gidana, muna tattaunawa ne, amma daga baya tattaunawar ta rikide zuwa gardama. A lokacin ne ta ɗauki wuƙa da niyyar soka mini,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa budurwar ta samu rauni a wuyanta yayin da suke kokawa kan wuƙar. A cewarsa, ya yi ƙoƙarin ceton ta bayan ta ji rauni, amma daga bisani ta mutu.
“Ban yi niyyar kashe ta ba. Na yi ƙoƙarin ceton ta bayan ta ji rauni, amma ta mutu,” in ji matashin.

Source: Original
'Yan sanda sun cafke matasa a Kano
A wani labarin kuma, kun ji cewa Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama wasu matasa biyu masu shekaru 19 bisa zargin mallakar makamin bindiga ba bisa ƙa’ida ba.
Jami'an na 'yan sanda sun kwato bindiga ƙirar Pistol da aka ƙera a gida tare da harsasai biyu masu rai daga hannun wadanda ake zargi.
Asali: Legit.ng
