InnalilLahi: An Shiga Jimami Bayan Rasuwar Jigon APC a Saudiya Yayin Aikin Hajji

InnalilLahi: An Shiga Jimami Bayan Rasuwar Jigon APC a Saudiya Yayin Aikin Hajji

  • An shiga jimami bayan jigon jam'iyyar APC ta riga mu gidan gaskiya a kasar Saudiyya wajen zuwa aikin hajji
  • Marigayiyar mai suna Ramota Bankole ta kasance jajirtacciya a jam'iyyar APC wanda ta rike mukamai da dama
  • Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran jami'yyar a jihar, Seye Oladejo ya fitar a yau Alhamis

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Makkah, Saudiyya - Hukumomi sun sanar da rasuwar wata Hajiya kuma jigon jam'iyyar APC a kasar Saudiyya.

Marigayiyar mai suna Ramota Bankole ƴar asalin jihar Lagos ta rasu a kasar yayin da ta je aikin hajji.

Jigon APC ta rasu a Saudiyya yayin aikin hajji
Jigon APC, Ramosa Bankole ta kwanta dama a Saudiyya. Hoto: All Progressives Congress, Inside the Haramain.
Asali: Facebook

Wane mukami Bankole ta rike a APC?

Kara karanta wannan

Ana daf da zabe, PDP ta sallami tsohon mataimakin gwamna da jiga-jiganta 2

Bankole kafin rasuwarta, ita ce tsohuwar sakatariyar jin dadi ta jam'iyyar APC a jihar Lagos, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sakataren yada labaran jami'yyar, Seye Oladejo shi ya tabbatar da haka a yau Alhamis 20 ga watan Yunin 2024, Vanguard ta tattaro.

"Rasuwarta ta zo mana bazata da kuma jimami, tabbas ta kasance jajirtacciya a jam'iyyar APC."
"Bankole ta kasance mai hidima ga APC wanda ta ke kokarin fadakar da mata kan shiga siyasa, Allah ya mata rahama."

- Seye Oladejo

Shugabar karamar hukuma ta yi jimami

Shugabar karamar hukumar Epe, Surah Animashaun ta yi jimamin rasuwar Bankole a yau Alhamis 20 ga watan Yunin 2024.

Animashaun ta ce marigayiyar lafiyarta kalau ta bar Najeriya zuwa kasa mai tsarki.

Ta tura sakon ta'aziyya ga iyalan marigayiyar da karamar hukumar Epe da ma jam'iyyar APC baki daya.

Kara karanta wannan

Ganduje ya ƙara rusa ƴan adawa, manyan jiga-jigai da dubban mutane 4450 sun koma APC

Alhaji daga Plateau ya rasu a Hajji

A wani labarin, kun ji cewa wani Alhaji da ya fito daga jihar Plateau, ya riga mu gidan gaskiya a ƙasa mai tsarki wajen gudanar da aikin Hajjin bana na shekarar 2024.

Sakataren hukumar jin daɗin Alhazai ta jihar, Alhaji Hayabu Dauda, ya tabbatar da rasuwar Alhajin mai suna Ismaila Musa, a birnin Makkah na ƙasar Saudiyya.

Alhaji Hayabu Dauda ya bayyana cewa Alhajin ya rasu ne a asibitin ƙwararru na Annur da ke birnin Makkah, inda ya shafe makonni uku yana jinya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.