Bayan APC Ta Buƙaci Cafke Shi, Kwankwaso Ya Tura Sako ga Tsohon Gwamna

Bayan APC Ta Buƙaci Cafke Shi, Kwankwaso Ya Tura Sako ga Tsohon Gwamna

  • Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya jajantawa tsohon shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki kan rasuwar mahaifiyarsa
  • Kwankwaso ya tura sakon ta'aziyya bayan rasuwar Florence Morenike Saraki a jiya Talata 18 ga watan Yuni 2024
  • Tsohon gwamnan jihar Kano ya yi addu'ar samun rahama ga marigayiyar tare da ba iyalanta hakurin wannan babban rashi da suka yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Jigon siyasar jihar Kano, Sanata Rabiu Kwankwaso ya tura sakon ta'aziyya ga Bukola Saraki.

Kwankwaso ya jajantawa Saraki kan rasuwar mahaifarsa a jiya Talata 18 ga watan Yuni 2024.

Kwankwaso ya jajantawa Saraki kan rasuwar mahaifiyarsa
Rabi'u Kwankwaso ya tura sakon ta'aziyya ga Bukola Saraki kan rashin mahaifiyarsa. Hoto: @bukolasaraki, @KwankwasoRM.
Asali: Twitter

Kwankwaso ya tura sakon ta'aziyya ga Saraki

Sanatan ya bayyana haka a yau Laraba 19 ga watan Yuni a shafinsa na X inda ya jajantawa iyalan marigayiyar.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya shiga babbar matsala, jam'iyyar APC ta nemi jami'an tsaro su kama shi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Marigayiya Florence Morenike Saraki ta rasu ne bayan fama da jinya kamar yadda tsohon shugaban Majalisar ya tabbatar.

Tsohon gwamnan Kano daga bisani ya yi addu'ar samun rahama a gare ta da yafiya daga Ubangiji madaukakin Sarki.

Ya kuma roki Allah ya ba iyalan marigayiyar hakurin jure wannan babban rashi da suka yi na uwa.

"Ina mika sakon ta'aziyya ga mai girma Bukola Saraki da iyalansa da kuma al'ummar jihar Kwara kan rasuwar Florence Morenike Saraki."
"Ina addu'ar ubangiji ya mata rahama ya kuma ba iyalanta hakurin jure wannan rashin da suka yi."

- Rabi'u Musa Kwankwaso

Mahaifiyar Bukola Saraki ta rasu

Wannan na zuwa ne bayan tsohon shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki ya sanar da rasuwar mahaifiyarsa.

Tsohon gwamnan Kwara, Saraki ya sanar da rasuwar Florence Morenike Saraki a jiya Talata 18 ga watan Yuni a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Allahu Akbar: Mahaifiyar tsohon shugaban majalisar dattawa ta rigamu gidan gaskiya

APC ta buƙaci cafke Kwankwaso kan kalamansa

A wani labarin, kun ji cewa jam’iyyar APC reshen jihar Kano, ta yi kira ga hukumomin tsaro da su gaggauta cafke Rabiu Kwankwaso.

An ruwaito cewa Rabiu Kwankwaso ya zargi Gwamnatin Tarayya karkashin jam’iyyar APC da kyankyasar sababbin ‘yan ta’adda a Kano.

Sanatan ya yi wannan zargi bayan tuge Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero amma ake ci gaba da ba shi tsaro a jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.