Ana Tsaka da Bikin Sallah Wasu Sun Hallaka 'Yar Gidan Magajiya, Zara a Dakin Otal

Ana Tsaka da Bikin Sallah Wasu Sun Hallaka 'Yar Gidan Magajiya, Zara a Dakin Otal

  • Rundunar 'yan sanda a Abuja ta cafke wasu mutane biyu kan kisan budurwa mai zaman kanta a dakin otal
  • Rundunar na zargin Maman Ajiya da Usman Lawal da caccakawa Zara Tua almakashi inda suka yi ajalinta
  • Kakakin rundunar 'yan sanda a Abuja, Joshephine Adeh ta tabbatar da faruwar lamarin inda ta ce an fara bincike

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Rudnunar 'yan sanda a birnin Abuja ta tabbatar da cafke wasu mutane kan kisan wata budurwa mai zaman kanta.

Wadanda ake zargin Maman Aliya da Usman Lawal sun dabawa budurwar mai suna Zara Tua almakashi a otal.

An cafke wasu da zargin kisan 'yar gidan magajiya a otal
An kama wasu mutane 2 da zargin kisan 'yar gidan magajiya a Abuja. Hoto: Nigeria Police Force.
Asali: Twitter

An cafke wasu da kisan 'yar magajiya

Kara karanta wannan

Hajji 2024: Hukumomin Saudiyya sun kwamushe mutum 18 bisa karya dokar aikin Hajji

Lamarin ya faru ne a otal din Galaxy Byazhin a ranar Lahadi 16 ga wata Yuni a Kubwa da ke birnin Abuja, cewar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana zargin daya daga cikinsu ne ya aikata laifin bayan ya shiga cikin otal din inda ya samu budurwar a ciki bayan samun sabani.

Wani mazaunin yankin kusa da otal din da ya bukaci boye sunansa ya ce budurwar ta kasance karuwa ce mai zaman kanta, cewar Sahara Reporters.

Majiyar ta ce an caka mata almakashi a wurare bakwai a jikinta har da cikinta inda 'yan sanda suka kwash ta zuwa asibiti.

'Yan sanda sun yi martani a Abuja

Kakakin rundunar 'yan sanda a birnin, Joshephine Adeh ta tabbatar da faruwar lamarin inda ta ce an fara bincike.

"An samu sabani tsakanin mutanen uku inda ya yi sanadin Zara wanda aka caccaka mata almakashi."

Kara karanta wannan

Kotu ta daure matashin da ya sace dabbobi, ya kalmashe kudin mutane a aljihu

"Bayan samun rahoton, rundunar 'yan sanda ta isa wurin inda ta samu matasa sun yiwa Ajiya duka kawo wuka.
"An kwashi Ajiya da kuma Zara zuwa babban asibitin Kubwa inda likitoci suka tabbatar da cewa Zara ta rasu."

Joshephine Adeh

'Yan sanda sun fusata a Kano

Kun ji cewa Rundunar 'yan sanda ta bayyana fushinta ga wadanda su ka yi ihu ga sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II ihu bayan ya dawo daga sallar idi.

Kamar yadda aka saba a al'ada, sarkin Kano kan sauya hanya bayan ya idar da sallar idi, a nan ne sarki Sanusi II ya bi ta Zage/Zango kuma a nan ne aka ji wasu na yi masa ihu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.