Daliba Ta Hallaka Jaririyarta Cikin Wani Yanayi Mara Dadi a Jigawa

Daliba Ta Hallaka Jaririyarta Cikin Wani Yanayi Mara Dadi a Jigawa

  • Wata ɗaliba mai karatu a jami'ar gwamnatin tarayya da ke Dutse (FUD) ta samu ƙaruwa bayan ta haifi ɗiya mace
  • Sai dai, ɗalibar da aka sakaya sunanta wanda take a aji biyu ta kashe jaririyar bayan ta jefo ta daga saman benen ɗakin kwanan ɗalibai mata a jami'ar
  • Rundunar ƴan sandan jihar ta tabbatar da aukuwar lamarin inda ta ƙara da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike kan mummunan lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Jigawa - Wata ɗaliba ƴar aji biyu (wacce aka sakaya sunanta) a jami’ar gwamnatin tarayya ta Dutse (FUD) da ke jihar Jigawa, ta salwantar da ran jaririyarta.

Ɗalibar ta yi wannan aika-aikar ne ta hanyar jefo jaririyar daga saman benen ɗakin kwanan ɗalibai mata.

Kara karanta wannan

Sojojin sama sun mayar da martani, sun halaka ƴan bindiga da yawa a Arewa

Daliba ta kashe jaririya a Kaduna
Daliba ta kashe jaririyarta a jihar Jigawa
Asali: Original

Yadda ɗaliba ta kashe jaririyarta a FUD

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Jigawa, DSP Lawan Shiisu Adam, ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa, cewar rahoton jaridar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kakakin ƴan sandan ya ce ɗalibar ta haifi jaririya sannan ta jefar da ita daga saman ɗakin kwanan ɗalibai wanda hakan ya sanya ta ce ga garinku nan.

DSP Lawan ya ce an garzaya da jaririyar zuwa asibitin koyarwa na Rasheed Shekoni da ke Dutse inda likitan da ke bakin aiki ya ba da tabbacin cewa ta rasu, rahoton The Punch ya tabbatar.

Me ƴan sanda suka ce kan lamarin?

"Bayanin da aka samu daga majiyoyi masu inganci sun nuna cewa wata ɗaliba ƴar aji biyu a jami’ar gwamnatin tarayya ta Dutse (FUD) ta haifi ɗiya mace."
"Daga nan kuma ta jefar da ita daga wani benen ɗakin kwanan ɗalibai mata, sakamakon haka jaririyar ta mutu nan take."

Kara karanta wannan

Atiku ya fadi babban mai laifi kan halin kuncin da ake ciki a Najeriya

"Tawagar ƴan sanda ta garzaya wurin da aka aikata laifin, inda suka kai jaririyar da mahaifiyarta zuwa asibitin koyarwa na Rasheed Shekoni Dutse, inda wani likita da ke bakin aiki ya tabbatar da mutuwar jaririyar."
"A halin yanzu, an kwantar da wanda ake zargin inda ake ci gaba da duba lafiyarta yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike."

- DSP Lawan Shiisu Adam

An tsinci gawar ɗaliba a Kano

A wani labarin kuma, kun ji cewa an tsinci gawar wata ɗalibar jami’ar kimiyya da fasaha ta Aliko Dangote da ke Wudil, Aisha Yahaya, a wani gidan kwanan ɗalibai da ke wajen makarantar.

Wasu daga cikin abokan karatunta da suka yi magana kan rasuwarta, sun danganta mutuwarta kan takurawa kai wajen karatu da fargabar jarrabawa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng