Hankula Sun Tashi Yayin da Sojan Najeriya Ya Salwantar da Ransa

Hankula Sun Tashi Yayin da Sojan Najeriya Ya Salwantar da Ransa

  • Wani jami’in sojan Najeriya ya salwantar da ransa har lahira a gaban ƙofar bataliya ta 144 ta rundunar sojoji (FOB) a jihar Abia
  • Jami’in sojan mai suna Vitalis wanda yake matsayin da CSM ya fito ne daga Okpuala a Ngor-Okpuala a jihar Imo da ke yankin Kudu maso Gabas
  • Mutuwar Vitalis ta girgiza abokan aikinsa inda ake sa ran zai yi ritaya a watan Oktoba na wannan shekara, kuma ba a gano musabbabin mutuwarsa ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Abia - Wani sojan Najeriya da ke aiki a jihar Abia ya aikata aika-aikar raba kansa da duniya.

Sojan wanda yake aiki da bataliya ta 144 Forward Operation Base (FOB) da ke High School Ngwa, Abayi, a ƙaramar hukumar Osisioma, ya salwantar da ransa.

Kara karanta wannan

"Ka yafewa maƙiya," Matasan Arewa sun aike da saƙo ga Sarki Aminu Ado Bayero

Sojan Najeriya ya salwantar da ransa
Sojan Najeriya ya salwantar da ransa a jihar Abia Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

Sojan mai suna Vitalis wanda ke da matsayin CSM, ɗan asalin Okpuala a Ngor-Okpuala a jihar Imo, ya harbe kansa a ƙofar FOB, cewar rahoton jaridar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa sojan ya salwantar da ransa

Ba a dai san dalilin da ya sa ya yanke wannan gurguwar shawarar ba saboda babu wata sanarwa da hukumomi suka fitar, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.

Wasu majiyoyi daga cikin jami’an tsaro a jihar sun bayyana cewa, bincike ne kawai zai gano ainihin abin da ya sanya ya ɗauki wannan matakin.

A cewar majiyoyi, har zuwa rasuwarsa babu wani batun yana fuskantar matsala a gidansa ko wurin aikinsa.

Bayanai kan sojan da ya salwantar da ransa

An tattaro cewa, sojan sai dai kawai aka neme shi aka rasa ba tare da sanin inda ya dosa ba.

Kara karanta wannan

Gwamna ya yi martani yayin da sojoji suka hallaka shugaban 'yan bindiga

Fiye da sati biyu da suka wuce ba a ji daga gare shi ba, domin abokan aikinsa da hukumomi sun kasa samunsa.

Daga nan kawai sai ya dawo sansanin sojojin sannan ya bindige kansa wanda hakan ya ba abokan aikinsa mamaki matuƙa.

Sojoji sun sheƙe ƴan ta'adda

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojoji na rundunar Operation Whirl Punch da bataliya ta musamman ta 198 ta sojojin Najeriya sun kashe ƴan ta’adda shida a jihar Kaduna.

Dakarun sojojin sun kashe ƴan ta'addan ne a wani samame da suka kai a ƙaramar hukumar Birnin Gwari ta jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng