Abun Al Ajabi
Wata mata ta shiga jirgi a Najeriya, lamarin da ya tada hankalinta tsabar cunkoso. An ga lokacin da take zabga ihun rashin samun iskan da za ta shakao a ciki.
Wani bidiyo ya nuna yadda wata budurwa ta gina gida domin huce haushin biyan kudin haya. Ta ce tana alfahari da mallakar gida mai daukar hankali irin wannan.
Wani bidiyo da ke yawo a dandalin soshiyal midiya ya nuno lokacin da wata budurwa ta kwace waya daga hannun wani soja sannan ta bige da yi masa rawa a nan take.
Wata dattijuwar mata da ke aiki a Walmart ta samu tallafin $100,000 daga wajen jama’a bayan bayyanar bidiyonta zaune ita kadai cikin kunci da damuwa a fuskarta.
Wani maciji ya jawo cece-kuce yayin da jama'a suka ga yana kokarin shiga bandaki zai buya. Jama'a sun ce wannan lamari ne babba, ya kuma ba su tsoro sosai.
Wata budurwa ta barar da sa'ar yin aurenta yayin da ta kama sana'ar karuwanci duk da kuwa saurayin na yi mata duk wani abin da take bukata. Bidiyo ya fallasa.
Wata matashiya yar Najeriya ta samu gagarumin kyauta daga wajen Ubangiji inda ya azurta ta da haihuwar yara biyar a lokaci guda, maza uku da kuma mata biyu.
An kama Fredrick Nwajagu, Eze Ndigbo na Ajao da ke jihar Lagas, wanda aka gani a wani bidiyo da ya yadu yana barazanar kawo yan IPOB jihar ta kudu maso yamma.
Wasu iyali da suka so amfani da sabon salo wajen bikin mutuwar kakarsu sun yi amfani da tukunya a matsayin akwatin gawa wajen kai ta makwancinta, an sha mamaki.
Abun Al Ajabi
Samu kari