Yara Manyan Gobe: Bidiyon Yaro Dan Watanni 7 Da Ya ‘Dare Tsani Cike Da Kwarewa Ya Ba Da Mamaki

Yara Manyan Gobe: Bidiyon Yaro Dan Watanni 7 Da Ya ‘Dare Tsani Cike Da Kwarewa Ya Ba Da Mamaki

  • Wani bidiyon yaro dan watanni bakwai yana hayewa saman tsani ya matukar baiwa mutane da dama mamaki
  • Karamin yaron ya kasance a filin wasa inda ya dungi hayewa sama da taimakon hannaye da kakafunsa
  • A bidiyon mai ban mamaki, yaron mai ji da karfi ya yi nasarar darewa saman tsanin sannan ya sauko kasa da kansa

Wasu iyaye suna da kasada kan yanayin wasannin da suke barin yaransu su yi ba tare da wani a kusa da su ba, musamman idan suna kanana.

Abun farin ciki ne ganin cewa yara sun girma cikin sauri sannan suna iya yawonsiu yadda suke so ba tare da wani babba ya bi sahunsu ba.

Karamin yaro yana hayewa saman tsani
Yara Manyan Gobe: Bidiyon Yaro Dan Watanni 7 Da Ya ‘Dare Tsani Cike Da Kwarewa Ya Ba Da Mamaki Hoto: @amenfi_black
Asali: TikTok

Wasu yaran su kan kasance da karfi sosai tun ma kafin su cika shekara daya a duniya kuma su kan yi abubuwansu cike da kuzari.

Kara karanta wannan

“Ki Je Ki Gwada a Bariki”: Budurwa Ta Kwace Waya Daga Hannun Soja, Bidiyon Ya Yadu

Wani yaro dan watanni bakwai ya yi wani abun mamaki a wajen wasa yayin da wani babba ke gefe yana kallonsa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yaron ya rarrafa da hannayensa biyu da kafafuwansa zuwa wajen wasan wanda ke dauke da wani dan karamin tsani a cikinsa.

Ya doshi inda tsanin yake sannan ya yi amfani da shi wajen tsayawa kan kafafunsa. Daga nan sai ya dungi hawa matattakalar da taimakon hanayye da kafafunsa, cikin kankanin lokaci sai ga yaron a saman tsanin.

Lokacin da ya kai sama, sai ya dara sannan ya kalli kewayensa wanda hakan ke nuna sam baya tsoro.

Har ila yau, yaron mai tarin wayo ya rarrafa ya sako kasa da taimakon hannayensa. Ya yi dukka wannan ba tare da taimakon wani babba ba.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

Kara karanta wannan

Kaman Almara: Wani Dan Najeriya Ya Yi Tafiya Kan Ƙwai Ba Tare Da Sun Fashe Ba, Bidiyon Ya Yaɗu

@Abenaempress 23 ya rubuta:

"Mai shirin zama fitinannen shugaban ajin makaranta."

@user9445614408512 ya yi martani:

"Ya yi kyau yaro."

@osikani_dee_barber ya yi martani:

"Gwarzon namiji."

@user446695103146 ya cika da mamaki:

"Wow!"

@wonder_tee_22 ya rubuta:

"Ina ganin dan portable ne, wahala wahala."

@titusishaku ta yi martani:

"Hazikin yaro mai wayo."

@nyiteera ta yi martani:

"Iyaye basu da tsoro ba zan iya bari ya hau sama haka ba."

Daga yanzu garin kwaki za ka sha: Uwa ta koka bayan danta ya zubar da madarar N16k

A wani labarin kuma, wata matashiyar mata ta garzaya soshiyal midiya don kokawa a kan halin da ta riski danta, yaron dai ya barnatar da madarar gwangwani da ta siya masa kan N16k.

Asali: Legit.ng

Online view pixel