Matashi Ya Siya Motar Benz, Ya Kashe Fiye Da Miliyan N37, Kwantena Ce Ta Kawo Ta

Matashi Ya Siya Motar Benz, Ya Kashe Fiye Da Miliyan N37, Kwantena Ce Ta Kawo Ta

  • Bidiyon wata motar Marsandi Benz GLE 53 da wani matashi ya siya ya haddasa cecekuce a soshiyal midiya
  • Mutumin wanda ya nunawa danginsa motar, ya shilla tsadaddiyar abar hawan a kefan wata tirela a kan titi
  • Mutane da dama sun tofa nasu kan nasarar da ya samu, yayin da wasu suka roki Allah ya inganta rayuwarsu

Wata kyakkyawar budurwa, @emprezforba, ta je shafin soshiyal midiya don wallafa bidiyon sabuwar mota kirar Marsandi da dan uwanta ya siya ya kuma nunawa danginsa.4

Yan uwar mutumin ta cika da farin ciki yayin da take zaune a cikin motar tare da sanya hannunta a kan sitiyarin. Sauran mutanen ma sun kasance a wajen domin taya shi murna.

Matashi da sabuwar motarsa a kwantena
Matashi Ya Siya Motar Benz, Ya Kashe Fiye Da Miliyan N37, Kwantena Ce Ta Kawo Ta Hoto: @emprezforba
Asali: TikTok

Matashi ya siya tsadaddiyar mota kirar Benz

Roban kasan ya nuna motar kirar Marsandi Ben GLE 53 ce. A cewar CarBuzz, farashin motar ya fara ne daga $102,600 (N47,229,858).

Kara karanta wannan

Yadda Karancin Naira Ya Kashe Kasuwancin Miliyoyin Mutane a ‘Yan Watanni – ASBON

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mutane da dama sun garzaya sashin sharhi na bidiyon don muhawara kan ko ya kashe miliyan N100 kan motar ko bai kashe ba. Masu amfani da TikTok sun sha mamaki.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@ironmonkey29 ya ce:

"Baaba benz din miliyan 100 da doriya, kun yi nifa fah."

@Michael :dizzy ya ce:

"Baaba benz din miliyan 100..gaba da gabanta."

@Victor Richard ya ce:

"Ina tayaka murna mai gida Allah ya kara arziki."

@@Explorer ya yi al'ajabi:

"A gefen tirela yake gudu."

@Na’imaaaaa ta ce:

"Kudi bai san kyawawan mutane ba."

@Collins Owusu ya ce:

"Ki fadawa dan uwanki ya nuna mana hanya."

@Draco_boy3800 ya ce:

"Dan uwa ya kuke yin abun ne. Ina dai tayaka murna."

@obh.ey ya ce:

"GLE mashin ne."

@Favour7 ta ce:

"Miliyan 100 wannan kudin jini ne, babu abun da za ku fada mani."

Kara karanta wannan

Dattijuwa Ta Samu Kyautar Fiye Da Miliyan N44 Bayan Yaduwar Bidiyonta Cikin Bakin Ciki

@TRUSTED ta ce:

"Yar'uwa ina so na zama kawarki."

Kasada adashin abu: Matashiya ta fisge waya a hannun soja, bidiyon ya ba da mamaki

A wani labari na daban, jaama'a sun cika da matukar mamaki bayan cin karo da bidiyon wata matashiyar budurwa da ta yi kasadar fisge waya daga hannun wani soja yana tsaka da magana da wani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel