Wata Uwa Ta Koka Kan Yadda Diyarta Ta Hargitsa Mata Gida, Ta Shige Durowa Ta Yi Zamanta a Bidiyo

Wata Uwa Ta Koka Kan Yadda Diyarta Ta Hargitsa Mata Gida, Ta Shige Durowa Ta Yi Zamanta a Bidiyo

  • Wata uwa da diyarta ta kaita iyaka ta nuna gajiwarta yayin da ta nadi bidiyon yadda ta hargitsa masu falo
  • Yarinyar ta shige cikin durowa sannan ta fito da komai na ciki, an gano wayoyi iri-iri baje a kasa
  • Iyaye da dama da suka kalli bidiyon yarinyar sun bayyana yadda suke fama da nasu yaran a gida

Wata uwa, @olamidoyin1722, ta wallafa bidiyon yadda diyarta ta sauya mata kamannin falonta sannan ta hargitsa komai da ke ciki.

Yarinyar ta isa durowan talbijin da ke falon sannan ta yi watsi da duk wasu wayoyi da ke ciki a kasa. Bidiyon ya nunota tana jawo durowan tare da zama a ciki.

Karamar yarinya tana hargitsa wuri
Wata Uwa Ta Koka Kan Yadda Diyarta Ta Hargitsa Mata Gida, Ta Shige Durowa Ta Yi Zamanta a Bidiyo Hoto: @olamidoyin1722
Asali: TikTok

Yayin da yarinyar ke ci gaba da hargitsa gidan, mahaifiyarta na ta daukar bidiyon yadda abun ke gudana. Yadda ta mayar da hankali kan abun da take yi zai nuna maka cewa tana jin dadin barnar da take yi ba da wasa ba.

Kara karanta wannan

Tir da talauci: An kirkiri motar da mutum zai iya kiranta a waya, kuma ta zo babu direba

Bidiyon ya tara martani fiye da 60 da 'likes' fiye da 1,500.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kalli bidiyon a kasa:

Iyaye sun bayyana halin da suke ciki da yaransu

Mutane da dama da suka yi sharhi a wallafar matar sun bayyana yadda suke fama da nasu yaran a gidajensu.

@Ayyub Adesegun ya ce:

"Yi hakuri halinsu kenan haka diyata ke dandanawa kowa kudarsa a gida."

@Bell's Treat ta ce:

"Ni da 'dana muna da daki da falo na musamman wanda ya banbanta da na mijina. Ya ce mu ne hawan jininsa."

@morufabiodun95 ta ce:

"Allah ya yi maki albarka."

@Silent Cash ta ce:

"Wannan kaka ce."

@Miide ta ce:

"Me ya hada yaran nan da wannan durowan shine inda 'dana ya fi jin dadin wasa."

@Ghostblogger101 ta ce:

"Dana ya dandana mani kudata."

@Easy touch ta ce:

Kara karanta wannan

“Za Mu Iya Kebewa?” Matashi Ya Hangi Kyakkyawar Budurwa a Gefen Mahaifiyarta, Ya Mika Mata Wasikar Soyayya

"Wallahi wannan kanwa Zeenat ce haka zeenat take zama a cikin durowa ita ma lokacin da take yarinya wadannan yaran ko."

@mhizz adejoke ta ce:

"Wannan shine aikin diyata kullun."

@MCjay2905 ya ce:

"Wannan shine abun da 'dana ke yi a kodayaushe, tuni durowan suka tashi aiki."

Da muka nemi jin ta bakin wata uwa mai yara hudu, Malama Khadija ta ce ai yara sai hakuri domin a cewarta wani lokacin da suka yi mata wani barnar sai ta ji kamar ta jefar da su ta huta.

Malama Khadija ta ce:

"Ba ki ji bahaushe ya ce yaro man kaza ba, ni fa kafin na yi aure idan na ji ance Allah ya kawo kazantar daki sai na yi ta mamaki don mutum ya mallaki da sai kazanta ya shigo kuma, ashe dai da gaske ne.
"Rannan haka na shiga makwabta kafin na dawo sai na tarar da autata Ihsan yar shekaru 2 ta shiga kicin ta farfasa mun kwai sannan ta debo gishiri ta afka a ciki. Kamar na jefar da ita na huta haka na ji amma ya mutum ya iya? Kyauta ce wani ma da kudi yana nema bai samu ba. Allah dai ya raya mana su yasa mu ci amfaninsu."

Kara karanta wannan

Hakimin mata: Mata ta gano mijinta zai kara aure, ta yashe kudin asusun hadin gwiwarsu

Bidiyon yaro yana hawa tsani ya ba da mamaki, watanninsa 7

A wani labarin kuma, mun ji cewa jama'a sun cika da mamaki bayan ganin bidiyon wani yaro dan watanni bakwai yana hawa tsani ba tare da taimakon wani ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel