“Babban Kasada”: Budurwa Ta Kwace Waya Daga Hannun Soja a Wani Bidiyo Da Ya Yadu

“Babban Kasada”: Budurwa Ta Kwace Waya Daga Hannun Soja a Wani Bidiyo Da Ya Yadu

  • Bidiyon wata matashiyar budurwa tana zolayar wani soja da kwace masa wayarsa ya haddasa cece kuce a soshiyal midiya
  • A bidiyon mai ban mamaki, budurwar ta fisge wayar daga hannun sojan sannan ta fara taka rawa yayin da shi kuma sojan ke kallonta cikin kaduwa
  • Bidiyon ya sa dandalin TikTok ya dauki dumi yayin da jama'a suka cika da mamakin wannan karfin hali nata

Wata matashiyar budurwa yar Najeriya ta wallafa wani bidiyo a TikTok tana mai nuna yadda ta zolayi wani jami'in soja wanda ke amsa kira a kan wayar tarho.

Matashiyar mai karfin hali ta fisge waya daga hannunsa ta baya sannan ta kama yi masa rawa a gaba.

Budurwa tana tsokanar wani soja
“Babban Kasada”: Budurwa Ta Kwace Waya Daga Hannun Soja a Wani Bidiyo Da Ya Yadu Hoto: @ajaissaxy
Asali: TikTok

A bidiyon, sojan ya cika da mamakin abun da ta aikata sannan ya tsaya yana kallon yadda take rawa yayin da take rike da wayarta.

Kara karanta wannan

Kaico: An debi 'yan kallo yayin da saurayi ya kama budurwa a otal tana karuwanci

Ta take magana kan abun da ta aikata, matashiyar ta bayyana cewa ta tsorata sosai yayin zolayar sojan wanda ke sanye da kayansa na aiki amma dai ta aikata hakan.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Bidiyon ya haifar da martani sosai daga wajen jama'a da ke ganin wannan zolayar a matsayin babban kasada suna masu jinjina mata a kan wannan karfin hali nata.

Jama'a sun yi martani

@Candy ta ce:

"Babu abun da za ku fada mani cewa yarinyar nan bata hadu da mutumin ba kafin wannan bidiyon."

@user7190102813981 ya rubuta:

"Tab don dai mace ce baka mazge ta ba da namiji ne da ka sha mazga."

@winnie ta yi martani:

"Wannan sojan na da kirki fa."

@Pretty girl doze ta yi martani:

"Ki yi tunani da wayan ya fadi daga hannunki bisa kuskure, chai jini zai zuba ba kadan ba."

Kara karanta wannan

Manyan Arewa Sun Fusata, Sun Aike da Muhimmin Sako Bayan Tinubu Ya Ci Zabe

@Tha barhbie276 ta ce:

"Kada ki gwada a cikin bariki."

@Holaidey ta yi martani:

"Bari wayar ta fadi a hannunki za ki san abun da muke kira da Shege promax."

@uchechi kenkwo ta ce:

"Babban kasada, ki yi tunanin da wayar ya fadi fa."

Kalli bidiyon a kasa:

Bidiyon yadda kamannin wata matashi ya sauya ya girgiza intanet

A wani labarin kuma, jama'a sun cika da mamaki a soshiyal midiya bayan cin karo da bidiyon sauyawar wani matashi daga kaura zuwa wani hadadden gaye.

Asali: Legit.ng

Online view pixel