Abun Al Ajabi
Wani fasto mai mata 2 ya hakura da yunkurinsa na auren mata ta uku. Faston wanda ya bayyana aniyarsa na auren mata ta 3 a baya ya bayyana dalilinsa na sauya tunani.
Wata matar aure ta haifi tagwaye kasa da awanni 24 bayan mijinta ya mutu. Bidiyon matar da yaran nata ya tsuma zukatan mutane da dama a soshiyal midiya.
Jami'an 'yan sanda sun yi nasarar kamo daliban firamare 2 da suka cinna wa makarantarsu wuta a jihar Ogun, rundunar ta ce ta fara bincike kan wannan danyen aiki.
Wani mutum da tsinci teba a kwali maimakon wayar iPhone 15 ya koka cikin kunar rai yayin da yake dudduba kwalin. Bidiyon ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya.
Wata jami’ar yar sanda ta yi fice a soshiyal midiya bayan ta rera taken kasa cike da kura-kurai a wani taron manyan jami’an yan sanda a jihar Imo.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi wa tagwayen da aka haifa a hade fatan nasara a tiyatar da za a yi masu yayin da suka bar Kano zuwa kasar Saudiyya don ayi masu aiki.
Jama'a sun shiga mamaki yayin da wani mutum ya hau jirgi da kudade, ya sako kudade daga sama a matsayin kyauta ga wadanda ke bibiyarsa a kafar yanar gizo.
Wani rasiti ya nuna yadda a baya a Najeriya ake biyan kudade kadan a jami'a, amma yanzu ake biyan makudan kudade a yanayin da kowa ke kokawa duba da tattali.
Yayin da ake ci gaba da kuka kan yadda aka kashe wata mata a Gombe, an kuma sake kashe wata mata a jihar Neja, an ce matar mai koyarwa ce a jami'ar FUT.
Abun Al Ajabi
Samu kari