Kowa Ya Tuna Bara Bai Ji Dadin Bana Ba, Tsohon Rasiti Ya Nuna Yadda Aka Biya N340 Kudin Makaranta

Kowa Ya Tuna Bara Bai Ji Dadin Bana Ba, Tsohon Rasiti Ya Nuna Yadda Aka Biya N340 Kudin Makaranta

  • Wani dan Najeriya ya janyo cece-kucen masu amfanin soshiyal midiya bayan ya yada bidiyon rasitin jami'arsa
  • Tsohon hoton da ya yada ya nuna cewa adadin kudin makaranta na shekara a jami’ar jihar Ribas a baya N340 ne kacal
  • Masu amfani da shafukan sada zumunta sun mayar da martani mai daukar hankali kan hoton, inda da dama suka bayyana ra'ayoyinsu game da halin da kasar nan ke ciki a yanzu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.

Najeriya - Wani tsohon hoton rasitin kudin makaranta da jami'ar jihar Ribas ta ba wani tsohon dalibinta, Henry Omoregie, ya yadu a kafar sada zumunta.

Henry Omoregie ya yada hoton a yanar gizo yayin da yake jaddada gagarumin sauyin da aka samu a tattalin arzikin Najeriya a cikin 'yan shekaru.

Kara karanta wannan

An shiga rudani yayin da aka tsince gawar Lakcara a jami'ar Neja, an mata yankan rago

Rasitin makaranta ya jawo cece-kuce
Yadda ake biyan kudin makaranta a baya | Hoto: Henry Omoregie
Asali: Facebook

Meye mutumin ya rubuta a yanar gizo?

Duba ga rasitin da aka ba dalibin a shekarun da suka gabata, jimillar kudaden shekarar karatu a wancan lokacin bai wuce N340 ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Henry ya yada hoton a Facebook tare da cewa:

"Naira 340 kacal kudin makaranta a jami'ar jiha (Rivers). Kudin karatu na a Jami'ar Tarayya Naira 10 ne kacal a wancan zamanin (Jami'ar Ibadan)."

Martanin jama’a a kafar sada zumunta

Masu amfani da kafar sada zumunta sun shiga sashen sharhi don bayyana ra'ayoyinsu game da wannan rasiti.

Esther ta ce:

"Kudin karatu ya karu a lokacin da na samu gurbin karatun digiri na biyu a 1992, duk da haka akwai araha. Kasa da Naira dubu 2 ne kuma na biya komai!"

Nosa Eke ya mayar da martani da cewa:

"Duba da farashin Dala, bai canza da yawa ba, ninka shi sau 1000, shikenan. 1000% na karin farashi. Mun kade."

Kara karanta wannan

Ya kamata CBN ta sa a daina amfani sabbin takardun Naira da Buhari ya kawo, malami ya fadi dalilai

Sammie ya ce:

"Lokacin da kasar ke cikin hayyacinta."

Evbota ya kara da cewa:

"Ka ga bambanci daga wancan lokaci zuwa yanzu. Dan uwa menene mafita? Najeriya ba za ta iya ci gaba a haka ba."

Dalibai za su rage karatu a Najeriya

A wani labarin, Shugaban Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU), Farfesa Emmanuel Osodeke ya bayyana cewa kaso 40 zuwa 50 za su watsar da karatu nan ba da jimawa ba.

Osodoke na magana ne kan karin kudin makarantu da Gwamnatin Tarayya ke yi a kasar inda ya ce nan da shekaru uku idan ba ta shawo kan matsalar ba, da yawa za su bar karatu.

Farfesan ya yi wannan gargadi ne yayin hira da gidan talabijin na Channels a Abuja a jiya Lahadi 24 ga watan Satumba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel