Farar Dabara: Yar Najeriya Na Sayar da Ganyen Ayaba a Turai, Tana Samun Makudan Kudade

Farar Dabara: Yar Najeriya Na Sayar da Ganyen Ayaba a Turai, Tana Samun Makudan Kudade

  • Wata yar Najeriya ta bayyana yadda take samun dubban nairori ta hanyar siyarwa mutane da ganyen ayaba a turai
  • Harkar ta fara ne bayan ta aika sakon imel zuwa wasu shagunan Afrika a kasar Afrika ta Kudu da Birtaniya, tana mai sanar da su dadin da ke cikin yin alale a ganyen ayaba
  • Daga tura imel, ta samu amsoshi masu kyau da harka sannan ta baje kolin dalolin da take samu a ciki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Wata yar Najeriya mai wayo, Ọlaedo Chiọma Irene, ta yi murnar samun kudaden shiga daga sana'ar siyar da ganyen ayaba a kasashen waje, yayin da take Najeriya.

A wata wallafa da ta yi a shafin Facebook a ranar Laraba, 1 ga watan Oktoba, Chioma ta wallafa hotuna da ke nuna yadda take hada ganyenayaban a cikin ledoji da kwalaye bayan ta ninke su da kyau.

Kara karanta wannan

Cin zarafi: Kungiyar NLC ta fadi ranar tsunduma yajin aiki, ta tura bukatu 6 ga gwamnati

Matashiya na siyar da ganyen ayaba
Farar Dabara: Yar Najeriya Na Sayar da Ganyen Ayaba a Turai, Tana Samun Makudan Kudade Hoto: Olaedo Chiọma Irene
Asali: Facebook

Yadda Olaedo Chioma Irene ta kama sana'ar ganyen ayaba

Da take bayanin yadda abun ya fara, Chioma ta ce ta fara aika sakon imel zuwa shagunan Afrika a kasashen kudu ta Afrika da Birtaniya sannan ta tallata masu ganyen ayaba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarta, ta yi masu bayanin dadin dake tattare da samun kwastamomi suna cin alale daga ganyen ayaba sannan ta yi masu bayani ta Zoom.

Ta ce yan matanta sun yi mata dariya. Sai dai kuma, a makon jiya, ta samu sakon imel daga daya daga shagunan turan, suna neman ganyen ayaba.

Chioma ta karfafawa mutane gwiwar cewa kada su karaya yayin da ta wallafa wani sakon ciniki da ke nuna yadda ta samu $450 (sama da N439k) kan ganyen alalenta. Chioma ta rubuta:

"Na aika sakon imel zuwa daya daga cikin shagunan Afrika a kasar Afrika ta kudu, UK sannan na samar da su...yin alale da ganyen ayaba.

Kara karanta wannan

A bar batun man fetur; Tinubu ya fadi inda Najeriya za ta koma samun kudin shiga

"Na yi bayanin dadin da ke tattare da samun kwastamomi suna ci da jin dadin alale da aka yi da ganye mai tsafta.
"Ranar da na yi bayani a zoom, yan matana na ta yi mani dariya.
"Don haka a makon jiya, na samu sakon imel daga shagon don tura ganyen alale.
"An gama ciniki.
"Ban taba yarda zan iya samun irin wannan kudi da gayen ayaba ba.
"Na saka wannan don karfafawa wani gwiwa ne, kada ki yanke kauna.
"Ni shaida ce."

Yan Najeriya sun yaba ma Ọlaedo Chiọma Irene

Omotayo Khareemah ta ce:

"Na tayaki murna
"Wannan abun mamaki ne, kina da hikima.
"Allah ya kara nasara."

Randy Sammy ya ce:

"Ganyan ayaban Naija ya rigani fecewa.
"Baaba ganyen ayaba ma ya samu martaba faaa."

Rita Ifunanya Obiemezie ta ce:

"Da farko, ke yar baiwa ce da kika yi tunanin wannan kasuwanci.
"Ina tayaki murna hajiya."

Nwafor Ijeoma Melody ta ce:

Kara karanta wannan

Matar aure ta nemi kotu ta datse igiyar aurenta bayan shekaru 2 babu haihuwa

"Na so yadda kika gyara abun zuwa wani mataki. Na tayaki murna."

Budurwa ta nemi lambar saurayi ba kunya

A wani labari na daban, wata mata ta garzaya dandalin TikTok don bayar da labari mai ban al'ajabi na yadda ta hadu da mai shirin zama mijinta da yadda ya nemi aurenta cike da shauki.

Wata mata mai suna @i_am_evelyn, ta bayyana cewa ita ce ta fara nuna tana ciki a lokacin da ta yi arba da shi sannan daga bisani ta nemi ya bata lambar wayarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel