Jama'a Sun Yiwa Dan Caca Kaca-Kaca Don Ya Ci N15m Ya Ba Wanda Ya Ba Shi Satar Amsa N100k

Jama'a Sun Yiwa Dan Caca Kaca-Kaca Don Ya Ci N15m Ya Ba Wanda Ya Ba Shi Satar Amsa N100k

  • Wani dan Najeriya ya sha caccaka a dandalin X kan bai wa wanda ya ba shi satar amsa N100k daga zunzurutun kudi naira miliyan 15.6 da ya ci
  • Hakan na zuwa ne bayan mutumin ya nuna takardar cacar da ya buga bayan nasarar da ya samu a cacar da ya buk=ga da N100 kacal
  • Sai dai kuma, mutane sun kare mutumin da ya taki sa'a, cewa ya yi kokari da ya saki N100k a matsayin tukwici

Wani matashi dan Najeriya ya sha suka a soshiyal midiya kan bai wa wanda ya ba shi satar amsa N100k kacal daga naira miliyan 15.6 da ya ci a caca.

A ranar Litinin, 30 ga watan Oktoba, mutumin ya garzaya dandalin X don baje kolin takardar nasarar da ya yi sannan ya yi jinjina ga wasu mutane biyu da ake tunanin wadanda suka ba shi satar amsa ne.

Kara karanta wannan

Watanni da kaddamarwa, rashin mai ya jawo Dangote bai fitar da litan fetur ba

Matashi ya lashe miliyan 15 a caca
Jama'a sun yiwa dan caca kaca-kaca don ya ci N15m ya ba wanda ya shi satar amsa N100k Hoto: Guardian, Lists
Asali: Twitter

Ya buga caca da N100 sannan ya ci zunzurutun kudi har naira miliyan 15.6. Awanni bayan nan, sai wani mai amfani da twitter, @CleanThing_, ya caccake shi yayin da yake taya shi murnar nasarar da ya samu.

Kamar yadda ya rubutun ya bayyana, bai kamata ace N100k kacal zai ba wanda ya ba shi satar amsa ba. Ya rubuta:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Na tayaka murna mutumina, amma lashe N15.6M daga cacar da aka buga da, da turawa wanda ya ba ka satar amsa N100k a matsayin tukwici, hmm… shin za mu iya yin fiye da haka a matsayin mutane."

Kalli wallafar a kasa:

Jama'a sun caccaki mutumin da ya soki wanda ya lashe miliyan 15 a caca

Sai dai kuma, jama'a sun kare dan cacan.

@MakeleleJersey ya ce:

"Dukkanku ba ku da godiyar Allah. Idan ya zabi kin tura komai fa. Tunda dan mutum baya faduwa a wasanku, sau nawa kuka mayarwa mutane da kudinsu."

Kara karanta wannan

Tinubu: Duk minista ko wani da ba zai iya tabuka komai ba, ya tafi ya ba ni wuri

@LytSkinnedGirl ta ve:

"Ina tare da shi ni dai, ka lashe N15.M daga cacar N100. Ka yanke shawarar kyautar da 100k, Bai yi ba kuma mugunta ce don Allah.
"Abun da ya kamata ace ya tura maka N15.5M sannan ya yi amfani da sauran 100k din wajen siyan data sannan ya dunga kallon hotunan WhatsApp dinka. barawo."

@Derah91 ya ce:

"Idan wasar ta tashi, za ka bayar da gudunmawar faduwar? Wani irin iko ne wannan? Ya kamata ya baka dukka ai."

Budurwa ta sharbi kuka a gidan caca

A wani labarin, wata matashiyar budurwa yar Najeriya mai suna @di_vine, ta koka a soshiyal midiya bayan ta rasa kudinta a harkar caca.

A cikin wani bidiyo da ya yadu a TikTok, an gano matashiyar tana kuka yayin da take yi wa kanta fada kan shiga harkar caca da ta yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel