Bola Tinubu
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya aike da sabon gargaɗi ga sojojin juyin mulkin Jamhuriyar Nijar. Shugaba Tinubu ya gargaɗi sojojin kan lafiyar Shugaba Bazoum.
Akwai yiwuwar Nyesom Wike zai koma Jam'iyyar APC daga PDP bayan ba shi Minista. Makomar sauran 'Yan G5 ba ta da tabbas tun da su ka yi fito na fito da jam'iyya.
Wata kungiyar arewa ta yi kira ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da majalisar dattawa da su gaggauta tabbatar da Mallam Nasir El-Rufai a matsayin minista.
Har yanzu tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai na iya zama minista a gwamnatin Shugaba Bola Tinubu. An bayyana cewa Tinubu ya warewa Nasir El-Rufai.
Daniel Bwacha wanda ya kasance na hannun daman dan takarar shugaban kasa a PDP, Atiku Abubakar ya soki yadda Shugaba Tinubu ya rarraba ma'aikatu ga ministoci.
Wasu matan aure a jihar Kaduna sun yi zanga-zanga kan tsadar abinci da kuma tsananin yunwa da ke damunsu, sun ce yara biyu sun mutu saboda tsabar yunwa a Igabi.
Wasu magidanta na satar kayyayakin gonar mutane don kai wa iyalansu a jihar Taraba, wasu manoman sun ce ganin halin da ake ciki ba su kai su kara ba ga hukumomi
Gwamnan jihar Neja Mohammed Umaru Bago, ya fara tunanin hawa kan teburin sulhu da ƴan bindiga, domin magance matsalar tsaron da ta daɗe tana addabar jihar.
Shugaba Bola Tinubu, ya bai wa 'yan Najeriya haƙuri kan halin matsi da suka samu kawunansu a ciki, biyo bayan cire tallafin man fetur da gwamnatinsa ta yi.
Bola Tinubu
Samu kari