Zargin Daukar Nauyin Ta’addanci Da Wasu Zarge-Zarge Da Ake Yi Wa Emefiele

Zargin Daukar Nauyin Ta’addanci Da Wasu Zarge-Zarge Da Ake Yi Wa Emefiele

  • Jerin zarge-zargen da ake yi wa dakataccen gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, sun bayyana
  • Wata majiya ta DSS ta bayyana cewa masu tambayoyi za su tsitsiye Emefiele kan zargin daukar nauyin ta'addanci, yin facaka a CBN da tattalin arziki da sauransu
  • Majiyar ta kuma bayyana cewa DSS na iya tunkarar kotu don samun wani umurni na tsare Emefiele

Abuja - Bayanai sun billo game da zarge-zargen da ake yi wa dakataccen gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele.

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da Emefiele a matsayin gwamnan CBN a ranar Juma'a, 9 ga watan Yuni.

Gwamnan CBN, Godwin Emefiele
Zargin Daukar Nauyin Ta’addanci Da Wasu Zarge-Zarge Da Ake Yi Wa Emefiele Hoto: Central Bank of Nigeria/ Muhammad B Muhammad
Asali: Facebook

Kamar yadda jaridar Punch ta rahoto, za a yi wa Emefiele, hadimansa da manyan daraktoci tambayoyi kan:

  • Basussuka na biliyoyin naira da aka baiwa manoma karkashin shirin Fadama
  • Takaddamar siyar da bankin Polaris
  • Zargin daukar nauyin kungiyar yan aware na Biafra (IPOB)
  • Zarge-zargen da ke kewaye da badakalar chanjin kudade

Kara karanta wannan

DSS Ta Jero 'Laifuffukan' Emefiele, Za Ta Bukaci Karin Lokacin Cigaba da Tsare Shi

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Jaridar ta rahoto cewa wata majiya a hukumar DSS ta bayyana cewar rundunar tsaron na sirri ya kuma shirya wata tawagar masu tambayoyi domin tsitsiye Emefiele kan wadannan zarge-zargen.

  • Zargin daukar nauyin ta'addanci
  • Facaka a CBN da tattalin arziki
  • Manufar sauya fasalin kudi da sauransu

Majiyar ta ci gaba da bayyana cewar DSS za ta tunkari kotu domin samun wani umurni na tsare Emefiele domin samun damar yi masa tambayoyi.

Tinubu ya dakatar da gwamnan CBN, Godwin Emefiele, ya yi umurnin bincike

A baya mun kawo cewa shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da Godwin Emefiele a matsayin gwamnan babban bankin Najeriya (CBN).

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktan labarai na ofishin babban sakataren gwamnatin tarayya, Willie Bassey ya fitar a ranar Juma'a, 9 ga watan Yuni.

Kara karanta wannan

A bar batun Emefiele: Jam'iyyar su Peter Obi ta fadi hukumar da ya kamata a bincika a Najeriya

Bai kamata Tinubu ya tsare Emefiele ba, Omokri

A wani labarin kuma, tsohon hadimin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, Reno Omokri, ya ce bai kamata gwamnatin Bola Tinubu ta kulle dakataccen gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Emefiele ba.

Omokri, a wata wallafa da ya yi a shafinsa na Twitter, ya ba gwamnati mai ci shawarar cewa kada ta fara zargin Emefiele ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel