Tinubu Na Daukar Matakan Da Suka Dace, Inji Sanata Ben Bruce

Tinubu Na Daukar Matakan Da Suka Dace, Inji Sanata Ben Bruce

  • Sanata Ben Murray-Bruce ya jinjinawa gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan yadda ta dauko aiki da daukar matakai don daidaita kasar
  • Tsohon Sanatan na Bayelsa ya bayyana cewar gwamnatin Tinubu na daukar matakan da suka dace
  • Murray-Bruce ya bukaci yan Najeriya da su zuba idanu su ga yadda tsohon gwamnan na jihar Lagas zai ingata kasar da tattalin arzikinta

Tsohon sanata wanda ya wakilci yankin Bayelsa ta gabas a majalisar dattawa, Ben Murray-Bruce, ya bayyana cewa shugaban kasa Bola Tinubu na daukar matakan da suka dace a gwamnatinsa.

A wata wallafa da ya yi a shafinsa na Twitter a ranar Juma'a, 9 ga watan Yuni, tsohon dan majalisar ya ce yan Najeriya su zuba ido su kalli gwamnatin Tinubu.

Shugaban kasa Bola Tinubu
Tinubu Na Daukar Matakan Da Suka Dace, Inji Sanata Ben Bruce Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

Murray-Bruce ya rubuta:

"Shugaban kasa Bola Tinubu na kira-kirayen da suka dace. Ya gyara Lagas ta zama mafi girman tattalin arziki na 6 a Afrika, sannan yanzu shine ke kula da ragamar tattalin arziki mafi girma a Afrika. Ku zuba ido ku yi kallo."

Kara karanta wannan

CBN ta zama ATM din munafukan gwamnati: Shehu Sani ya bi ta kan korarren gwamna Emefiele

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Martanin Bruce na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban kasar ya dakatar da gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele.

Tsauraran matakan da Tinubu ya dauka tun bayan hawa mulki

Tun bayan rantsar da shi a matsayin shugaban kasa a ranar 29 ga watan Mayu, Shugaban kasa Bola Tinubu ya dauki wasu tsauraran matakai ciki harda cire tallafin man fetur tun daga wajen da ya yi jawabin rantsar da shi.

Kwatsam kuma sai ga labarin cire Emefiele daga matsayin gwamnan babban bankin kasar a daren ranar Juma'a, 9 ga watan Yuni.

Bayan dakatar da shi, sai rundunar tsaron farin kaya wato DSS ta kwamushe shi domin gudanar da wasu bincike a kansa.

A wata sanarwa da ta fitar a ranar Asabar, 10 ga watan Yuni, hukumar DSS ta tabbatar da cewar dakataccen gwamnan na CBN yana tsare a hannunta yan awanni bayan ta karyata batun.

Kara karanta wannan

Godwin Emefiele: Wike Ya Yi Martani Ga Hukuncin Tinubu Na Dakatar Da Gwamnan CBN

Bai kamata gwamnatin Tinubu ta kulle Emefiele ba, Omokri ya ba sabuwar gwamnati shawara

A wani labarin kuma, tsohon hadimin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, Reno Omokri, ya ce bai kamata gwamnatin Bola Tinubu ta kulle dakataccen gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Emefiele ba.

Omokri, a wata wallafa da ya yi a shafinsa na Twitter, ya ba gwamnati mai ci shawarar cewa kada ta fara zargin Emefiele a bainar jama'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel