Ranar Dimokuradiyya: Dalilai 5 Da Suka Sa Ranar 12 Ga Watan Yuni Ke Da Muhimmanci A Tarihin Najeriya

Ranar Dimokuradiyya: Dalilai 5 Da Suka Sa Ranar 12 Ga Watan Yuni Ke Da Muhimmanci A Tarihin Najeriya

Ba za a ba da tarihin Najeriya ba tare da an ambaci ranar 12 ga watan Yuni ba, wacce muhimmiyar rana ce da al’ummar Najeriya suka yi fatan samun kyakkyawan sauyin shugabanci.

Rana ce mai cike da ɗumbin tarihi da ta kasance kowane ɗan Najeriya na tunawa da ita a zuciyarsa.

Hakan dai na da alaƙa da irin gwagwarmayar da 'yan Najeriya suka sha wajen fafutukar tabbatar da dimokuraɗiyya, bayan shafe shekaru da dama a ƙarƙashin mulkin gwamnatocin soji na kama-karya.

Abubuwa 5 da ke nuna muhimmancin ranar 12 ga watan Yuni
Janar Ibrahim Badamasi Babangida ne ya soke zaben Abiola na ranar 12 ga watan Yuni. Hoto: STR/AFP, Francois-Xavier HARISPE/AFP and PA Images
Asali: Getty Images

'Yan Najeriya a ranar sun yi fitar ɗango wajen kawar da gwamnatin sojoji ta hanyar zabar farar hula, MKO Abiola a matsayin shugaban ƙasa.

Legit.ng ta tattaro muku wasu dalilai guda biyar da suka sa ranar 12 ga Yuni ke da matuƙar muhimmanci a tarihin Najeriya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Abubuwa 4 Da Emefiele Ya Yi Da Suka Bata Wa Tinubu, Gwamnoni, Da Sauran 'Yan Najeriya Rai

1. Zaben shugaban ƙasa na 1993

A ranar 12 ga watan Yunin 1993 ne Najeriya ta gudanar da zaben shugaban ƙasa, wanda ake yi wa kallon ɗaya daga cikin mafiya inganci a tarihin ƙasar. Zaɓen dai ya samu gagarumar fitowar masu ƙaɗa kuri'a daga ko ina a faɗin Najeriya.

Marigayi Cif Moshood Kashimawo Olawale (MKO) Abiola, wanda fitaccen ɗan kasuwa ne, ya kasance wanda ya lashe zaɓen, inda ya samu gagarumin goyon baya daga ‘yan Najeriya da suka yi imani da manufarsa ta inganta ƙasar.

2. An samu hadin kan 'yan ƙasa

Kafin zuwan Bola Tinubu da Kashim Shettima da tikitin Muslim-Muslim, MKO Abiola shi ne ɗan siyasa na farko da ya fara aiwatar da irin wannan tsarin.

Abiola ya zaɓi tsohon jami'in diflomasiyya daga yankin Arewa maso Gabas, Baba Gana Kingibe a matsayin mataimakinsa.

Sai dai banbancin tsarin na Tinubu, Shettima da na Abiola da Kingibe shi ne, hadin kan 'yan Nijeriya a lokacin ba tare da lura da ƙabilanci, addini, ko bangaranci ba.

Kara karanta wannan

Dakarun Sojin Sama Sun Yi Luguden Kan Maboyar 'Yan Boko Haram a Borno, Sun Sheke Manyan Kwamandoji Da Yawa

Miliyoyin 'yan Najeriya sun ajiye saɓanin da ke tsakaninsu domin kaɗa kuri'unsu ga shugaban da suke ganin zai kawo musu sauyi a wancan lokacin.

3. Fafutukar neman dimokuraɗiyya

Soke zaɓen na 12 ga watan Yuni da gwamnatin mulkin soja ƙarƙashin jagorancin Janar Ibrahim Badamasi Babangida ta yi ya haifar da tarzoma da tashe tashen hankula a fadin kasar.

'Yan Najeriya daga sassa daban-daban sun fito kan tituna, suna neman a basu zaɓin dimokuraɗiyyar da suka yi.

Gwagwarmayar da 'yan ƙasa suka yi a lokacin ta nuna irin yadda suka zaƙu da su samu sauyi daga mulkin kama karya, zuwa mulkin farar hula mai 'yanci da walwala.

4. Rawar da Cif MKO Abiola ya taka

Cif MKO Abiola, wanda ake kyautata zaton shine ya lashe zaɓen 12 ga watan Yuni, ya zama wani babban madubi a dimokuraɗiyyar Najeriya.

Ya tsayu tsayin daka tare da ‘yan Najeriya wajen fafutukar ƙwato ‘yancinsu na dimokuraɗiyya daga hannun sojoji.

Kara karanta wannan

Muhimman Abubuwa 5 Da Ya Kamata Shugaba Tinubu Ya Yi Domin Ceto Nijeriya Daga Halin Da Take Ciki

Sai dai daga ƙarshe gwamnatin soji ta lokacin, ta kama Abiola gami da tura shi gidan yari, inda daga bisani ya rasu a can.

5. Dawowa mulkin dimokuraɗiyya da batun mayar da 12 ga Yuni ranar dimokuraɗiyya

Bayan wasu 'yan shekaru a mulkin soja, Najeriya ta samu dawowa kan tafarkin dimokuraɗiyya a ranar 29 ga Mayu, 1999.

Sannan a ranar 6 ga watan Yunin 2018 a ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari, Gwamnatin Najeriya ta amince da ranar 12 ga watan Yuni a matsayin ranar dimokuraɗiyya.

Gwamnati ta dai yanke wannan mataki ne domin muhimmantar da zaɓen ranar 12 ga watan Yunin 1993 da kuma abubuwan da suka biyo bayansa, tare da jinjinawa tsayin daka da sadaukarwar da 'yan Najeriya suka yi a fafutukar tabbatar da dimokuraɗiyya.

Muhimman abubuwan da Tinubu ya faɗa a jawabinsa na ranar dimokuraɗiyya

A labarin Legit.ng na baya, ta tattaro muku muhimman batutuwa guda biyar da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi taɓo a cikin jawabinsa na ranar dimokuraɗiyya.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Ɗumi: Muhimman Kalaman da Gwamnonin G5 Suka Faɗa Wa Shugaba Tinubu Sun Bayyana

A cikin jawabin nasa, Shugaba Tinubu ya yabi matar MKO Abiola, wato Kudirat Abiola, da Pa Alfred Rewane da kuma marigayi Shehu Musa Yar’Adua.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng