DSS Ta Jero 'Laifuffukan' Emefiele, Za Ta Bukaci Karin Lokacin Cigaba da Tsare Shi

DSS Ta Jero 'Laifuffukan' Emefiele, Za Ta Bukaci Karin Lokacin Cigaba da Tsare Shi

  • Bisa dukkan alamu Godwin Emefiele ya ga ta kan shi domin DSS ba ta da niyyar fito da shi a yanzu
  • Hukumar DSS ta yi ram da Gwamnan bankin CBN, kuma za a iya neman karin lokaci wajen tsare shi
  • Garkame Emefiele da aka yi zai ba jami’ai damar masa tambayoyi a binciken da ake gudanarwa

Abuja - Hukumar DSS ta na iya zuwa kotu a ranar Talata mai zuwa domin samun izinin cigaba da tsare Godwin Emefiele da aka dakatar daga CBN.

A rahoton Punch, an fahimci jami’an tsaron za su roki kotu ta amince masu tsare Godwin Emefiele na lokaci mara adadin domin ayi bincike da kyau.

Wata majiya a DSS ta shaida cewa hakan zai taimaka wajen yi wa gwamnan na CBN tambayoyi a kan zargin laifuffukan da ake yi masa da aikatawa.

Kara karanta wannan

Emefiele: Jerin Zarge-Zargen Da Ake Yi Wa Dakataccen Gwamnan CBN Yayin da DSS Ta Yi Sabon Yunkuri

Godwin Emefiele
Gwamnan CBN, Godwin Emefiele Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Za a iya shiga gidan Godwin Emefiele

Bayanai na nuna cewa akwai yiwuwar DSS ta shiga gidan dakataccen Gwmanan babban bankin kasar, tayi masa ta-tas domin samun hujjojin binciken.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wani jami’in da yake aiki da DSS ya fadawa jaridar an dade ana bibiyar Emefiele, kuma tun da ya shigo hannu, zai yi wahala ya samu ‘yancinsa da wuri.

Wannan jami’i ne yake cewa har kotun tarayya aka je domin samun izinin cafke shi, don haka watakila a binciki gida da ofishin Gwamnan na bankin CBN.

Zargin da DSS ta ke yi masa

Daga cikin zargin da ake yi wa Emefiele shi ne ya bada gudumuwa wajen ta’addanci a Najeriya, sannan ana tuhumarsa da facaka a karkashin tsarin NSIP.

Gwamnatin Muhammadu Buhari ta fito da shirin NSIP da nufin inganta rayuwar marasa galihu tun daga matasa, mata, masu kananan sana’a da dalibai.

Kara karanta wannan

Abubuwa 4 Da Emefiele Ya Yi Da Suka Bata Wa Tinubu, Gwamnoni, Da Sauran 'Yan Najeriya Rai

Rahoton ya ce ana zargin gwamnan CBN ya tafka badakala a karkashin tsarin noma da gwamnatin tarayya ta fito da shi, aka yi sama da kudin gwamnati.

Halin da ake ciki a yanzu

Har zuwa yammacin jiya, babu kowa a gidan Mista Emefiele da ke unguwar Maitaima a Abuja, haka zalika babu jami’an tsaro da aka hanga a gidan.

Haka lamarin yake a hedikwatar CBN, sam babu wasu ‘yan sanda masu fararen kaya illa jami’an da ke tsare da babban bankin da aka dakatar da gwamnanta.

An nada Gwamnan riko

A baya kun samu rahoto cewa Folashodun Adebisi Shonubi shi ne wanda zai gaji Godwin Emefiele har zuwa lokacin da za a gama binciken da ake yi.

A shekarar 2018 Shonubi ya zo CBN, kafin nan ya yi aiki Ecobank, Union Banki, Citi Bank da FCMB. Jama'a su na ta surutu ganin asalinsa Injiniya ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel