Bola Tinubu
Kotun koli ta sanar da ranar Litinin a matsayin ranar da za ta yanke hukuncin zaben shugaban kasa tsakanin Shugaba Tinubu da Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP.
Shugaba Bola Tinubu ya yi sabbin nade-nade har guda takwas a ma'aktar yada labarai ta kasa a yau Laraba, hukumomin sun hada da NOA da NTA da NAN da sauransu.
Ministan Abuja, Nyesom Wike ya bai wa Sakataren hukumar FCDA sa'o'i 24 don samo tsarin da za a bi na biyan diyya yayin da ake shirin rushe masallacin Abuja.
Sheikh Ahmad Gumi ya bayyana ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, a matsayin shaidanin mutum kan tarban ambasadan Isra’ila a Najeriya a ofishinsa.
Tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya ce maganar da Sheikh Ahmad Gumi ya yi na kiran Nyesom Wike da shaidani abu ne da ba za a amince da shi ba.
Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya zargi gwamnatin Bola Ahmed Tinubu da yaudarar Arewa da sunan tikitin Musulmi da Musulmi, ya caccaki Nyesom Wike.
Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya sanya labule da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, a fadar shugaban ƙasa a ranar, Laraba, 18 ga watan Oktoba.
Akwai talakawan da ke karkashin tsarin CCT wanda za a rika aika masu N5000. Gwamnatin tarayya ta ci bashin $800m daga bankin Duniya domin rage radadi.
APC ta yi raddi ga Babachir David Lawal wanda ya ce Peter Obi ya ci zaben 2023. Duk da Bola Tinubu aka ayyana a matsayin wanda ya lashe takarar, shi bai yarda ba.
Bola Tinubu
Samu kari