Abin da Mu ka Tattauna da Tinubu a Aso Rock - Shugabar WTO, Okonjo-Iweala

Abin da Mu ka Tattauna da Tinubu a Aso Rock - Shugabar WTO, Okonjo-Iweala

  • Ngozi Okonjo-Iweala ta samu damar ganawa da shugaban Najeriya a fadar Aso Rock a Abuja
  • Shugabar kungiyar ta WTO ta yi wa manema labarai bayanin abin da ya kai ta wajen Bola Tinubu
  • Tsohuwar Ministar tattalin arzikin ta ce WTO za ta cigaba da taimakawa mata, matasa da yara

Abuja - Darekta Janar ta kungiyar kasuwancin Duniya watau WTO, Ngozi Okonjo-Iweala ta yi bayanin zuwanta wajen Bola Ahmed Tinubu.

This Day ta rahoto Dr. Ngozi Okonjo-Iweala ta na mai cewa shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya san halin wahalar da jama’arsa ke ciki.

A yayin da ta ke yi wa ‘yan jarida jawabi a fadar shugaban kasa da ke birnin Abuja, tsohuwar Ministar ta fayyace dalilin zuwanta Aso Rock.

Bola Tinubu a Fadar shugaban kasa
Ngozi Okonjo-Iweala ta hadu da Bola Tinubu Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Meya kai Ngozi Okonjo-Iweala wajen Bola Tinubu?

Okonjo-Iweala ta ce ba komai ya kai ta wajen shugaba Bola Tinubu ba illa ganin yadda za ta taimaka wajen rage wahalar da ake ciki a Najeriya.

Kara karanta wannan

Orire Agbaje: Bayanin ‘Yar Jami’ar da ta Shiga Muhimmin Kwamitin da Tinubu ya kafa

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugabar ta WTO ta ke cewa mafi yawan zantawarsu ta kare ne kan yadda za a samar da ayyukan yi, tallafawa mata kuma a inganta kasuwanci.

"Gaskiya wannan ba tafiyar WTO ba ce, amma mun iya tattaunawa da Mai girma shugaban kasa game da irin tsare-tsaren da za a fito da su.
Mun yi magana game da yadda za a kawo manufofin al’umma da za su samar da ayyukan yi ga matasa, kuma su taimakawa mata da yara."

- Ngozi Okonjo-Iweala

An rahoto tsohuwar Ministar ta na cewa yara da mata su ka fi shan mafi yawan wahalar da ake ciki, inda Gwamnati ta sha alwashin kawo sauki.

WTO za ta taimakawa Gwamnatin Tinubu

A tattaunawar ne aka fahimci nau’in taimakon da gwamnatin Najeriya za ta bukata daga WTO.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Cusa 'Yar 400L a Jami'a a Kwamitin Gyaran Tattalin Arzikin Najeriya

"Yanzu haka mu na aiki da Najeriya musamman da mata da ke kanana da matsakaitan kasuwanci, mu na kokarin inganta masu kayansu.

Ko a harkar gona ne, tufafi da sauran wurare, domin su rika saida kayan na su a kasashen Duniya."

-Ngozi Okonjo-Iweala

Farfesa Muhammad Ali Pate wanda ya yi rakiya, ya shaida cewa shugaba Bola Tinubu ya san wahalar da ake ciki, kuma ya na kokari kawo sa’ida.

Shugaban ƙasa ya kebe da mutum 2

Tun a jiya aka samu rahoto Bola Ahmed Tinubu yana ganawa da Darekta Janar ta ƙungiyar kasuwanci ta duniya a fadar shugaban ƙasar.

A wajen taron kuma akwai Farfesa Muhammadu Ali Pate, tsohon ƙaramin minista wanda ake yi wa hangen Ministan kiwon lafiya a yanzu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel