Majalisa Ta Mika Jerin Sunayen Mutane 45 Da Aka Tabbatar Matsayin Ministoci Ga Tinubu

Majalisa Ta Mika Jerin Sunayen Mutane 45 Da Aka Tabbatar Matsayin Ministoci Ga Tinubu

  • Sunayen mutane 45 daga cikin 48 da aka tabbatar a matsayin ministoci sun isa ga Tinubu
  • Babban mai taimakawa shugaban ƙasar kan harkokin Majalisar Dattawa, Abdullahi Gumel ne ya bayyana hakan
  • Ya ce tun daren ranar Litinin, 7 ga watan Agusta ya hannanta sunayen mutanen da aka tabbatar ga Shugaban ƙasa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Babban mataimaki na musamman ga shugaban ƙasa kan harkokin Majalisar Dattawa, Abdullahi Gumel, ya miƙa sunayen mutane 45 da aka tabbatar a matsayin ministoci ga Shugaba Tinubu.

Gumel ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a Abuja ranar Talata kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

An miƙa sunayen ministoci ga Shugaba Tinubu
An miƙa sunayen mutane 45 da aka tantance matsayin ministoci ga shugaban ƙasa. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

An tabbatar da ministoci 45 cikin 48 da Tinubu ya tura majalisa

A ranar Litinin ɗin da ta gabata ne dai Majalisar Dattawan Najeriya ta tabbatar da ministoci 45 cikin 48 da Shugaba Tinubu ya aika ma ta.

Kara karanta wannan

Sunayen Ministocin Tinubu 2 Da Aka Tabbatar Duk Da Suna Da Wata Babbar Matsala a Tattare Da Su

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Majalisar ta cire sunayen mutane uku da ta dakatar da batun tabbatarwar ta su, saboda wasu ƙorafe-ƙorafe da aka shigar a kansu.

Mutane ukun da ba a tabbatar da su ba su ne tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai, Sanata Abubakar Danladi da kuma Stella Okotete.

Kamar yadda gidan talabijin na Channels ya wallafa, Stella Okotete na fuskantar ƙalubale ne saboda matsaloli a takardun karatunta.

Ya fadi dalilin Tinubu na nada ministoci 48

Gumel ya bayyana cewa, tun ranar Litinin, da misali 11:30 na dare ne ya hannanta sunayen tabbatattun ministocin ga shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa.

Ya kuma miƙa ɗumbin godiyarsa ga mambobin Majalisar Dattawa, saboda a cewarsa sun tabbatar da ministocin ba tare da wata doguwar jayayya ba.

Ya ƙara da cewa abinda ya rage yanzu shi ne, a saurari shugaban ƙasa domin ya tabbatarwa da kowanensu ma'aikatar da aka tura shi.

Kara karanta wannan

Majalisar Dattawa Ta Fitar Da Sabbin Bayanai Kan El-Rufai Da Sauran Ministocin Tinubu 2 Da Ba a Amince Da Su Ba

Ya kuma bayyana cewa akwai yiwuwar a raba wasu ma'aikatun da suka cika girma zuwa gida biyu, wanda hakan ne ya sa shugaban zai naɗa ministoci 48.

Tinubu ya yi wa 'yan Arewa riga da wando - Abdulaziz Abdulaziz

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan kalaman da mai taimakawa Shugaba Tinubu kan harkokin jarida, Abdulaziz Abdulaziz ya yi, na yaba ma sa kan yadda ya bai wa 'yan Arewa muƙamai.

Abdulaziz ya ce idan aka yi la'akari da mutanen da aka ba da sunayensu matsayin ministoci, za a ga cewa 'yan Arewa sun fi 'yan kowane yanki yawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng

Online view pixel