Bola Tinubu
A ranar Juma’a 3 ga watan Nuwamba ne fadar shugaban kasa ta bayyana cewa Faransa za ta dawo da dala miliyan 150 da tsohon shugaba, Janar Sani Abacha ya sace.
Gwamnatin Shugaba Tinubu ta shirya ceto 'yan Najeriya miliyan 50 daga kangin talauci, kamar yadda Ministar Ministar jin kai, Betta Edu ta bayyana
Babbar jam’iyyar adawar Najeriya ta Peoples Democratic Party (PDP) reshen jihar Akwa Ibom ta dauki matakin doka a kan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
Kungiyar Kwadago a Najeriya, NLC ta bayyana shiga yajin aikin gama-gari a ranar Laraba 8 ga watan Nuwamba idan har ba a sake Joe Ajaero ba da ke tsare.
Majalisar dokokin tarayya sun mika kuka ga shugaban kasa Bola Tinubu kan yadda Giwaye daga Kamaru ke shiga jihar Borno suna lalata amfanin gona a kowacce shekara.
Ya na da wahala dan siyasa ya daga hannun yaronsa ya ba shi mulki ba tare da an samu matsala a tsakaninsu ba, a yau, Fubara da Wike daga Ribas sun shiga wannan layi.
Gwamnonin jam'iyyar PDP sun jaddada goyon bayansu ga yunƙurin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, na tsoma baki a rikicin siyasar da ya ɓarke a jihar Ribas.
Ministan Abuja, Nyesom Wike ya amince da ware makudan kudade don gyara da kuma kula da masallacin Abuja da kuma cibiyar Kiristoci da ke birnin Tarayya Abuja.
A karshen makon nan aka ji labari Dala ta na karyewa a kasuwar canji tun da babban bankin Najeriya ya fara sallamar bankuna bashin kudin waje da su ke bi.
Bola Tinubu
Samu kari