Murna Yayin da Faransa Za Ta Dawo da Makudan Kudin da Abacha Ya Sace

Murna Yayin da Faransa Za Ta Dawo da Makudan Kudin da Abacha Ya Sace

  • Faransa ta yi alkawarin dawo da dala miliyan 150 da tsohon shugaban mulkin soja, Janar Sani Abacha ya sace
  • An tabbatar da wannan ci gaban ne a ranar Juma'a, 3 ga watan Nuwamba, lokacin da Shugaban kasa Bola Tinubu ya tarbi jakadan Shugaba Emmanuel Macron a fadar villa
  • Cike da jin dadin wannan labari, shugaba Tinubu ya yi alkawarin cewa gwamnatin tarayya za ta yi amfani da kudaden ta hanyar da ta dace

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Abuja - Fadar shugaban kasa ta sanar a ranar Juma'a, 3 ga watan Nuwamba, cewa kasar Faransa za ta dawo da dala miliyan 150 da tsohon shugaban mulkin soja, Janar Sani Abacha ya sace.

Kara karanta wannan

‘'Gwamnatin Tinubu za ta tsamo 'yan Najeriya miliyan 50 daga kangin talauci,’' Betta Edu

Shugaban kasa Bola Tinubu ya nuna jin dadinsa ga matakin da Faransa ta dauka yayin ganawarsa da ministar harkokin Turai da harkokin wajen Faransa Catherine Colonna.

Faransa zata dawo da kudin da Abacha ya sace
Murna Yayin da Faransa Zata Dawo da Makudan Kudin da Abacha Ya Sace Hoto: NESG
Asali: Twitter

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai, Ajuri Ngelale ya fitar/

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce shugaba Tinubu ya yaba da yadda ake kyautata alaka tsakanin Najeriya da Faransa, inda ya bayyana irin ci gaban da aka samu tun ziyarar da ya kai birnin Paris bayan hawansa mulki.

Ya jaddada muhimmancin inganta hadin gwiwa a harkokin siyasa da tattalin arziki tare da maraba da hadin gwiwarsu kan sauyin yanayi, hadewar tattalin arziki, ilimi, da al'adu.

Ya ce:

“Na gode da albishir kan dawo da kudin da Abacha ya sace. Muna godiya da hadin kanku game da dawo da kudaden Najeriya. Za a yi amfani da su yadda ya kamata wajen cimma manufofin ci gabanmu."

Kara karanta wannan

Gwamnonin PDP sun yi fatali da tsagin Atiku, sun koma goyon bayan shugaba Tinubu kan abu 1 tak

Najeriya da Faransa sun rattaba hannu kan yarjejeniyar €100m don bunkasa masana'antar sadarwa

Tinubu ya sanar da rattaba hannu kan wata yarjejeniya ta yuro miliyan 100 don tallafawa shirin i-DICE na Najeriya, wanda ke inganta saka hannun jari a masana'antar fasahar sadarwa da fasahar sadarwa (ICT) da masana'antar kere-kere.

Ministan sadarwa,kere-kere da fasahar zamani, Dr. 'Bosun Tijani, da ministar harkokin Turai da harkokin wajen Faransa ne suka rabbata hannu a yarjejeniyar.

Ministan na Faransa ta mika sakon fatan alheri na Shugaba Emmanuel Macron tare da bayyana aniyar Faransa na fadada hadin gwiwarta da Najeriya a bangarori daban-daban.

Ta kuma mika goron gayyata ga shugaban kasa Bola Tinubu domin halartar taron kungiyar zaman lafiya na birnin Paris mai zuwa.

Dangane da kudin da Abacha ya sace, jakadar shugaban kasar na Faransa ta yi bayanin cewa an kammala bin tsarin doka wajen dawo da kudin,

Ta ce:

"Tsari ne mai tsawo, amma mun yi farin ciki cewa an kammala shi. Wani lokaci, adalci yana iya zuwa da jinkiri, amma wannan babbar nasara ce.

Kara karanta wannan

A bar batun man fetur; Tinubu ya fadi inda Najeriya za ta koma samun kudin shiga

Ban taba sata ba, Hamza Al-Mustapha

A wani labarin, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Action Alliance (AA), Hamza Al-Mustapha ya ce bai taba satar kudi ba, sai dai ya kare dukiyar kasar duk da matsin lamba da wasu suka yi masa.

Al Mustapha ne babban dogarin tsohon shugaban Najeriya na mulkin soja, marigayi Janar Sani Abacha daga 1993 zuwa 1998.

Asali: Legit.ng

Online view pixel