Juyin Mulki: Tinubu Ya Bayyana Dabarun da Yake Amfani da Su Domin Kauce Wa Zubar da Jini a Nijar

Juyin Mulki: Tinubu Ya Bayyana Dabarun da Yake Amfani da Su Domin Kauce Wa Zubar da Jini a Nijar

  • Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana dabarun da yake bi domin kaucewa rikici a Jamhuriyar Nijar
  • Tinubu ya ce yana amfani da ɓoyayyun dabaru domin kaucewa zubar da jini a makwabciyar ƙasar nan
  • Ya ƙara da cewa Najeriya na sanya ido kan lamarin tare da binciko hanyoyin diflomasiyya domin warware matsalar

Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum da nishaɗi

Fadar shugaban ƙasa, Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana yadda ya sanya shugabannin ƙungiyar ECOWAS, shawo kan fushinsu kan juyin mulkin da aka yi a Jamhuriyar Nijar.

Tinubu ya ce yana amfani da dabaru domin kaucewa zubar da jini a makwabciyar ƙasar nan.

Shugaba Tinubu ya yi magana kan juyin mulkin Nijar
Shugaba Tinubu ya yi magana kan dabarun da yake amfani da su wajen magance rikicin Nijar Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Ya bayyana haka ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin ministar Turai da harkokin wajen ƙasar Faransa, Catherine Colonna, a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja a ranar Juma’a, 3 ga watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

Zaben gwamnoni: Shugaba Tinubu ya mika tutocin APC ga Ododo, Uzodinma da Sylva, bayanai sun fito

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Cif Ajuri Ngelale, mashawarci na musamman ga shugaban ƙasa kan harkokin yaɗa labarai da wayar da kan jama'a ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da aka sanya a shafin yanar gizo na fadar shugaban ƙasa.

Tinubu na sa ido kan juyin mulkin Nijar

Shugaba Tinubu ya bayyana cewa ƙasar na sa ido kan halin da ake ciki a jamhuriyar Nijar, da kuma binciko hanyoyin diflomasiyya.

A kalamansa:

"Muna da abokin aiki kuma shugaba da aka zaba ta hanyar dimokuradiyya, Shugaba Bazoum, ana amfani da shi a matsayin garkuwar ɗan adam. Idan ba mu yi taka tsan-tsan ba, shi da iyalinsa za su iya fuskantar haɗari."
"Na yi amfani da duk dabarun da suka dace domin guje wa zubar da jini a Jamhuriyar Nijar. Mun fahimci burin mutanenmu, ba sa son yaƙi, amma hakan ba ya nufin ba za mu iya ɗaukar ƙwaƙƙwaran mataki ba."

Kara karanta wannan

"Yaran Tinubu ne": Atiku ya caccaki gwamnonin PDP bisa shiga tsakani a rikicin Wike, Fubara

Shugaba Tinubu Ya Kunyata Janar Tchiani

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ƙi yarda su zauna domin tattaunawa da shugaban gwamnatin sojojin Jamhuriyar Nijar, Janar Abdourahamane Tchiani.

Janar Tchiani ya so ya gana da Shugaba Tinubu ne a ƙoƙarin da yake na ganin ya samu karɓuwa tun bayan kifar da gwamnatin Shugaba Mohamed Bazoum.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng