Gwamnonin PDP Sun Yi Fatali da Tsagin Atiku, Sun Koma Bayan Shugaban Tinubu Kan Abu 1 Tak

Gwamnonin PDP Sun Yi Fatali da Tsagin Atiku, Sun Koma Bayan Shugaban Tinubu Kan Abu 1 Tak

  • Gwamnonin jam'iyyar PDP sun bayyana dalilinsu na mara wa shugaban ƙasa Tinubu baya kan rikicin siyasar jihar Ribas
  • A cewarsu, saɓanin tunanin masu sukar hakan wanda ke tare da Atiku, tsoma bakin Tinubu ya zama wajibi kuma dole a yaba masa
  • Wannan na zuwa ne yayin da Ministan Abuja ya ce ba ruwansa da harkokin mulkin Ribas amma zai kare tsarin siyasar da aka kafa a 2015

Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Gwamnonin jam'iyyar PDP sun jaddada goyon bayansu ga shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, kan yunkurinsa na shiga tsakani a rikicin siyasar jihar Ribas.

Gwamnonin PDP sun kare kansu kan goyon bayan Tinubu.
Rikicin Rivers: Dalilin da Ya Sa Muke Goyon Bayan Bola Tinubu, Gwamnonin PDP Hoto: thenation
Asali: UGC

Sun bayyana cewa ƙungiyar gwamnonin Najeriya 36 (NGF) ta ƙagara ta ga an samu masalaha a rigimar wacce ta shiga tsakanin gwamna Similanayi Fubara da Nyesom Wike.

Kara karanta wannan

Wike Ya Zauna da ‘Yan Majalisa, Ya Jaddada Sharudan Sasantawa da Gwamnan Ribas

A cewarsu, tsoma baki da nufin sasanta rikicin wanda shugaban ƙasa ya kudiri aniya ya zama tilas domin guje wa yaɗuwar matsalar zuwa wasu jihohin, The Nation ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A nasa ɓangaren Ministan Abuja, Nyesom Wike ya ce ba shi da dalilin da zai sa ya yi katsalandan a harkokin mulkin Rivers, domin ya yi wa al’ummarta hidima na tsawon shekaru takwas.

Ya ci gaba da cewa babban abin da ya takaita a kai shi ne kare tsarin siyasar da aka gina tun shekarar 2015 a jihar Ribas.

Gwamnonin PDP sun jero dalilansu na goyon bayan Tinubu

Shugaban kungiyar Gwamnonin PDP kuma Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya kare tsoma bakin da Shugaba Tinubu ya yi a rikicin.

Saɓanin yadda wasu jiga-jigan da ke tare da Atiku Abubakar ke ikirarin cewa goyon bayan Tinubu na iya tarwatsa PDP, Bala ya ce yunƙurin ya yi daidai da ajendar NGF.

Kara karanta wannan

A Ƙarshe, Gwamnan APC ya tona gaskiyar abinda ya sa Shugaban NLC na ƙasa ya ci dukan tsiya a Imo

Darakta Janar na ƙungiyar gwamnonin PDP, CID Maduabum, shi ne ya faɗi haka a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce matakin da gwamnan Bauchi ya dauka abin alfahari ne.

Ya kara da cewa shiga taakanin da Tinubu ya yi a Ribas da rashin tsoma bakinsa a cikin shari’ar kotunan zabe abin yabawa ne, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Sanarwan ta ce:

"Dukkan gwamnonin jihohi 36 sun goyi bayan yunƙurin, musamman Shugaban ƙungiyar Gwamnonin PDP, Bala Mohammed, ya nuna goyon bayansa ga matakin Tinubu na shiga tsakani."

Kotu ta umurci a saki Emefiele

A wani labarin kuma Wata Kotu a babban birnin tarayya Abuja ta bada umarnin gaggauta sakin tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele.

Ta ce a sake shi ba tare da gindaya masa wasu sharuɗɗa ba, inda ta umarci EFCC da shugaban hukumar su aiwatar da wannan umarni.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262