Jerin Sunayen Gwamnoni da Suka Yi Wa Iyayen Gidansu a Siyasa Karan-Tsaye

Jerin Sunayen Gwamnoni da Suka Yi Wa Iyayen Gidansu a Siyasa Karan-Tsaye

A yau an wayi gari da labarin kokarin tsige gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara watanni biyar kacal da hawa karagar mulki.

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

A kullum samun matsala tsakanin Gwamna da uban gidansa da ya mika ma sa mulki na kara karuwa a Najeriya saboda dalilai da dama.

Jerin gwamnonin da ba su kare lafiya da iyayaen gidansu ba a siyasa
Ana yawan samun matsala tsakanin uban gida da yaransa a siyasa. Hoto: Bola Tinubu, Nyesom Wike, Siminalayi Fubara.
Asali: Facebook

Amma ba kowa ne zai iya cewa za a samu matsala tsakanin tsohon gwamnan Ribas, Nyesom Wike da Gwamnan mai ci Siminalayi Fubara ba.

Legit Hausa ta tattaro muku jerin gwamnaonin da su ka raba gari da iyayen gidansu:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Fubara da Wike

Watanni biyar kacal da karbar mulki a hannun uban gidansa, Fubara ya shiga matsala wacce za ta iya sanadin mulkinsa.

Kara karanta wannan

Gwamnonin PDP sun yi fatali da tsagin Atiku, sun koma goyon bayan shugaba Tinubu kan abu 1 tak

A jiya Lahadi 29 ga watan Oktoba rikicin ya fara bayan cinna wa wani bangare na majalisar dokokin jihar wuta.

Da safiyar yau Litinin ce kuma rikicin ya kara kamari yayin da majalisar ta tube shugaban ma su rinjaye don samun saukin tsige Fubara.

2. Ganduje da Kwankwaso

Tsawon lokaci Rabiu Kwankwaso na dasawa da Abdullahi Ganduje a matsayin yaronsa wanda ke ma sa biyayyya.

Ganduje ya yi mataimakin Kwankwaso har sau biyu a 1999 zuwa 2003 da kuma 2011 zuwa 2015 kafin lamura su dagule.

Hawan Ganduje kujerar gwamna a 2015 ke da wuya komai ya taarbare a tsakaninsu inda yaran Kwankwaso ke zargin Ganduje ya walakanta su yayin tantance kwamishinoni.

Bayan lalacewar alaka, Kwankwaso ya tsayar da Abba Kabir a matsayin gwamna a 2019 yayin da Ganduje ya yi nasara kafin sake tsayar da Abba a 2023 don tunkarar yaron Ganduje, Nasiru Gawuna.

Kara karanta wannan

Rundunar 'yan sanda: Abin da yasa jami'anmu suka watsa wa gwamna ruwan zafi da barkonon tsohuwa

3. Ambode da Tinubu

Tun bayan barin ofis a 2007, Tinubu ya kasance mai juya akalar wanda zai zama gwamnan a jihar tun daga Babatunde Fashola da Akinwumi Ambode da kuma Gwamna mai ci Babajide Sanwo-Olu.

Ambode ya fara samun matsala tun 2019 da ya ke neman zarcewa inda ake zargin ya bata wa wasu dattawan jam’iyyar rai wanda Tinubu ke tare da su.

Ambode ya fitar da makaman yakinsa inda ya yi zaben fidda gwani da wanda Tinubu ya tsayar takara amma bai ci nasara ba, cewar Nairaland.

4. Obaseki da Oshiomole

Godwin Obaseki wanda yaron Oshiomole ne ya shiga yaki da uban gidansa wanda ya ba shi mukami a lokacin mulkinsa, Daily Trust ta tattaro.

Oshiomole ya daga hannun Obaseki a 2016 a inuwar jam’iyyar APC kafin komai ya tabarbare cikin kankanin lokaci da kuma koma wa jam’iyyar PDP da Obaseki ya yi a kokarin neman zarcewa.

Kara karanta wannan

"Ba matsala ne ba idan an samu rashin jituwa tsakanin ɗa da mahaifi", Gwamna Fubara

Fubara ya yi martani kan yunkurin tsige shi

Kun ji cewa, Gwamna Siminalayi Fubara ya yi martani bayan kokarin tsige shi da mambobin majalisar jihar su ka yi.

Fubara yayin da ya ke jawabi ga ‘yan jihar, ya ce babu laifin da ya yi da ya cancanci wannan rashin mutunci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel