Bola Tinubu
Gwamnan jihar Ogun ya bayyana cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu zai kaddamar da kamfanin sarrafa auduga mafi girma a jihar Ogun. Mutane 250,000 za su samu aiki.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya ce Najeriya ba za ta saduda, ta sunkuyawa masu yunkurin tayar da hankali ba, ya ce gwamnatinsa na inganta walwar sojoji.
Kungiyar ta Afenifere ta yi magana kan zaben 2027 inda ta bayyana goyon bayanta ga shugaban kasa, Bola Tinubu ya kammala shekaru takwas a mulkin kasa.
Yayin da Remi Tinubu ke gudanar da shirin tallafawa mata, wasu sun fita daga wajen taron tallafa musu da ake yi karkashin matar shugaban kasa a Port Harcourt.
Yayin da ake shirin haɗaka a zaben 2027 da ke tafe, jam’iyyar LP ta ce ba za ta shiga kowace irin kawance ba kafin zaben 2027 domin kifar da Bola Tinubu.
Shugaban CAN na ƙasa ya nesanta kansa da kalaman shugaban CAN na Arewa, wanda ya kare Seyi Tinubu daga zargin da ake yi masa na tarwatsa taron dalibai.
Hukumomin FBI da DEA da ke Amurka sun nemi karin kwanaki 90 don fitar da takardun bincike kan zargin Tinubu, amma Greenspan ya nemi a fitar da su cikin mako guda.
Gwamnonin jihohin da APC ke mulki sun karyata jita jitar da aka yada cewa za su juya baya ga Bola Tinubu a zaben 2027. An yi zargin cewa za su hade da Atiku.
Hakeem Baba-Ahmed ya bukaci Atiku Abubakar da Shugaba Tinubu da su hakura da takara a 2027, su ba matasa dama su kawo sababbin dabaru don kawo babban ci gaba a kasa.
Bola Tinubu
Samu kari