Majalisar dokokin tarayya
Wani kudirin doka da ke neman kafa wata jiha a shiyyar Kudu maso Gabas ya tsallake karatu na farko a zauren majalisar wakilai. Za a rika kiran ta da 'Jihar Orlu'.
Majalisar wakilai ta bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya tsaurara matakan tsaro bayan an yawaita kai hari gidajen gyaran hali da guduwar fursunoni.
A ranar Alhamis ne majalisar wakilai ta umarci kwamitinta kan da’a da alfarma da ya binciki Hon. Ikenga Ugochinyere, bisa zargin bata sunan majalisar.
Majalisar dattawa ta amince da nadin Emomotimi Agama a matsayin babban daraktan hukumar hada-hadar hannayen jari (SEC). Shugaba Bola Tinubu ne ya gabatar da bukatar.
Wata kungiya mai rajin inganta shugabanci na gari ta Patriotic Volunteers for Good Governance ta shawarci ‘yan majalisu kan hanyar da za su bi wurin taimakawa kasar.
Mai magana da yawun majalisar wakilai, Hon. Akin Rotimi, ya ce kungiyoyin kwadago suna zuzuta albashin 'yan majalisun tarayya domin harzuka 'yan Najeriya.
Majalisar dattawan Najeriya ta nemi gwamnati ta dauki tsattsauran mataki kan iyayen dake barin yaransu na gararanba a kan titi maimakon zuwa makaranta.
Mambobin kungiyar ma’aikatan majalisar dokokin Najeriya (PASAN), reshen kungiyar NLC, sun katse ruwa da wuta na ginin a yajin aikin da 'yan kwadagon suka fara.
A wani yunkuri na dakile shirin yajin aikin da aka shirya yi a fadin kasar nan, majalisar tarayya da shugabannin kungiyoyin kwadago sun gana a Abuja.
Majalisar dokokin tarayya
Samu kari