Majalisar dokokin tarayya
Fadar shugaban kasa ta musanta rahotannin da ke yawo kan cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai yi jawabi ga 'yan majalisun tarayya a ranar Laraba.
Majalisar Dattawa ta amince da dokar dawo da tsohon taken Najeriya "Nigeria We Hail Thee" tare da maye gurbin "Arise O Compatriots" domin kara kishin kasa.
Yayin da gwamnatin Kano ta nemi alfarma wurin Bola Tinubu, shugaban ya yi biris, zai yi jawabi a taron majalisun Tarayya biyu kan nasarar dimukradiyya.
Yayin da ake ci gaba da dambarwa kan sarautar Kano, tsohon hadimin shugaban majalisar dokokin jihar, Hassan Cikinza Rano ya bayyana cewa an tafka kura-kurai.
'Dan majalisar ttarayya, Alex Ifeanyi Mascot Ikwechegh ya bar addinin da yake yi, ya zama musulmi kamar yadda wani ya yada a dandalin sada zumunta a karshen mako.
'Yan majalisar dokokin jihar Cross Rivers sun dauki matakin tsige kakakin majalisar daga kan mukaminsa. Ana zarginsa da tafka almundahanar kudade.
Wasu daga tsofaffin jami’an ‘yan sandan Najeriya sun gudanar da zanga-zangar lumana a babban birnin tarayya Abuja domin bayyana korafinsu na biyansu hakkokinsu.
A yau Talata majalisar dokokin jihar Rivers mai goyon bayan Gwamna Siminalayi Fubara ta tsara tantance waɗanda za su maye gurbin kwamishinonin Nyesom Wike.
Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Abba Kabir Yusuf ta gwangwaje yan majalisar jihar da motocin kece raini guda 41. An sayi kowace Toyota Fortuner a kan ₦68m.
Majalisar dokokin tarayya
Samu kari